دَلَائِلُ الْخَيْرَاتِ
Alamomin Alkhairai
Ha
اَلنِّيَّةُ | Intentions
اَللَّهُمَّ إِنِّي نَوَيْتُ بِالصَّلَوٰةِ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ امْتِثَالاً لِّأَمْرِكَ وَتَصْدِيقًا لِنَبِيِّكَ مُحَمَّدٍ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمَحَبَّةً فِيهِ وَشَوْقًا إِلَيْهِ وَتَعْظِيمًا لِّقَدْرِهِ وَلِكَوْنِهِ أَهْلاً لِّذَلِكَ
Ya Allah, hakika na yi niyyar yin salati ga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) domin biyayya ga umarninka da gaskata Annabinka Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da soyayya gare shi da kwaɗayin gamuwa da shi, da girmama darajarsa, da kuma kasancewarsa wanda ya cancanci hakan
فَتَقَبَّلْهَا مِنِّي بِفَضْلِكَ وَإِحْسَانِكَ وَأَزِلْ حِجَابَ الْغَفْلَةِ عَنْ قَلْبِي وَاجْعَلْنِي مِنْ عِبَادِكَ الصَّالِحِينَ.
Saboda haka Ka karɓe shi daga gare ni da falalarka da kyautatawarka, Ka kuma yaye labulen gafala daga zuciyata, Ka sanya ni a cikin bayinka sãlihai
اَللَّهُمَّ زِدْهُ شَرَفًا عَلَىٰ شَرَفِهِ الَّذِيٓ أَوْلَيْتَهُ. وَعِزًّا عَلَىٰ عِزِّهِ الَّذِيٓ أَعْطَيْتَهُ.
Ya Allah, Ka ƙara masa ɗaukaka a kan ɗaukakarsa wadda Ka sanya masa, da buwaya a kan buwayarsa wadda Ka ba shi
وَنُورًا عَلَىٰ نُورِهِ الَّذِي مِنْهُ خَلَقْتَهُ وَأَعْلِ مَقَامَهُ فِي مَقَامَاتِ الْمُرْسَلِينَ. وَدَرَجَتَهُ فِي دَرَجَاتِ النَّبِيئِينَ.
Da kuma haske a kan haskensa wanda Ka halicce shi daga gare shi, Ka ɗaukaka matsayinsa a cikin matsayoyin manzanni, da darajarsa a cikin darajojin annabawa
وَأَسْئَلُكَ رِضَاكَ وَرِضَاهُ يَا رَبَّ الْعَالَمِينَ. مَعَ الْعَافِيَةِ الدَّآئِمَةِ وَالْمَوْتِ عَلَى الْكِتَابِ وَالسُّنَّةِ وَالْجَمَاعَةِ وَكَلِمَتَيِ الشَّهَادَةِ عَلَىٰ تَحْقِيقِهَا مِنْ غَيْرِ تَبْدِيلٍ وَّلَا تَغْيِيرٍ.
Kuma ina roƙonka yardarka da yardarsa ya Ubangijin talikai, tare da afiya madauwami da mutuwa a kan Littafi da Sunnah da haɗin kan al’umma, da kalmomin shahada guda biyu a kan tabbatar da su ba tare da canzawa ko juyawa ba
وَاغْفِرْ لِي مَا ارْتَكَبْتُهُ بِفَضْلِكَ وَجُودِكَ وَكَرَمِكَ يَآ أَكْرَمَ الْأَكْرَمِينَ.
Ka yafe mini abin da na aikata na zunubai da falalarka da kyautarka da karamcinka, ya Mafi karamcin masu karamci
وَصَلَّى اللَّهُ عَلَىٰ سَيِّدِنَا مُحَمَّدٍ خَاتَمِ النَّبِيِّينَ وَإِمَامِ الْمُرْسَلِينَ. وَعَلَىٰٓ ءَالِهِ وَصَحْبِهِ أَجْمَعِينَ. وَسَلَامٌ عَلَى الْمُرْسَلِينَ. وَالْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Muhammadu, cikon annabawa kuma jagoran manzanni, da iyalansa da sahabbansa baki ɗaya, amincewa ta tabbata ga manzanni, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai