قُلْتُ لَمَّا غَابَ عَنِّي
Na Ce Lokacin Da Ya Ɓace Mini
Ha
قُلْتُ لَمَّا غَابَ عَنِّي
نُورُ مَرَاكَ الْمَصُون
Na ce sa'adda ya fake daga gare ni
hasken kyawunki kiyayye
شَفَّنِي وَاللَّهِ سُقْمٌ
فِيهِ قَدْ ذُقْتُ الْمَنُونَ
Na rantse da Allah, wata cuta ta cinye ni
wadda a cikinta na ɗanɗani mutuwa kanta
وَعُيُونِي مِنْ نَحِيبٍ
جَارِيَاتٌ كَالْعُيُون
Idanuna saboda kuka mai zafi
suna kwarara kamar maɓuɓɓugar ruwa
وَجُفُونِي مَا كَفَاهَا
مَا جَرَى حَتَّى جَفُون
Fatar idona ba ta gamsu da abin da ya kwarara ba
har sai da su kansu suka bushe
هَامَ قَلْبِي زَادَ وَجْدِي
فَمَتَى وَصْلَكْ يَكُونُ
Zuciyata tana gantali, begena yana ƙaruwa
to yaushe ne saduwarmu za ta kasance?
غَابَ عَنْ عَيْنِي ضِيَاهَا
يَا قَمَرَ دَارِي الْعُيُون
Haske ya gushe daga ganina
ya kyakkyawan Wata, ka sanyaya wa waɗannan idanun rai