مَلَكَنِي هَوَاكُمْ عَذَّبَنِي
Soyayyarku ta mallake ni, ta azabtar da ni
Ha
Ha
الـلَّـهْ الـلَّـهْ الـلَّـهْ الـلَّـهْ يَـا مَـوْلَانَـا
لَا بُـدَّ مِـن فَـنَـاء الْـمُـلْـكُ يَـبْـقَـى لِـلَّـه
Allah, Allah, Allah, Allah, ya Shugabanmu!
Lallai akwai karewa, mulki kuma ya tabbata ga Allah
مَـلَـكَـنِـي هَـوَاكُـمْ عَـذَّبَـنِـي
وَزَادَنِـي شَـوْقًا وَ قَـلَـقَا
Soyayyarku ta mallake ni, ta kuma azabtar da ni
Ta kuma kara mini shauki da rashin natsuwa
الـلَّـهْ الـلَّـهْ الـلَّـهْ الـلَّـهْ يَـا مَـوْلَانَـا
لَا بُـدَّ مِـن فَـنَـاء الْـمُـلْـكُ يَـبْـقَـى لِـلَّـه
Allah, Allah, Allah, Allah, ya Shugabanmu!
Lallai akwai karewa, mulki kuma ya tabbata ga Allah
الْـنَّـوَى وَالْـبَـيْـنُ أَقْـلَـقَـنِـي
وَغَـشِـيَ الْـقَـلْـبُ وَ إِحْـتَـرَقَ
Nisan gari da rabuwa sun tayar mini da hankali
Zuciya kuma ta lullube, ta kuma kone kurmus
الـلَّـهْ الـلَّـهْ الـلَّـهْ الـلَّـهْ يَـا مَـوْلَانَـا
لَا بُـدَّ مِـن فَـنَـاء الْـمُـلْـكُ يَـبْـقَـى لِـلَّـه
Allah, Allah, Allah, Allah, ya Shugabanmu!
Lallai akwai karewa, mulki kuma ya tabbata ga Allah
بِـثَـوْبِ رِضَـاكُـمْ كَـفِّـنُـونِـي
بِـبَـابِ حِمَاكُمْ أَلْـحِـدُونِـي
Da tufafin yardarku ku yi mini likafani
A bakin kofar gidanku ku binne ni
الـلَّـهْ الـلَّـهْ الـلَّـهْ الـلَّـهْ يَـا مَـوْلَانَـا
لَا بُـدَّ مِـن فَـنَـاء الْـمُـلْـكُ يَـبْـقَـى لِـلَّـه
Allah, Allah, Allah, Allah, ya Shugabanmu!
Lallai akwai karewa, mulki kuma ya tabbata ga Allah
وَاكْـتُـبُـوا عَـلَى قَـبْـرِي وَرَقَـةْ
هَـذَا مُـحِـبٌّ قَـدِ احْـتَـرَقْ
Kuma ku rubuta a kan kabari na wata takarda
Wannan masoyi ne wanda shauki ya kone shi