مَا مَعِي وَجَهْ قَابِل بِهْ سِوَى حُسُنْ ظَنِّي
Ba ni da fuskar da zan fuskance Ka da ita sai kyakkyawan zatona gare Ka.
Ha
مَا مَعِي وَجَهْ قَابِل بِهْ سِوَى حُسُنْ ظَنِّي
فِيكْ يَا رَبِّ فَارْحَمْنِي وَلَا تَمْتَحِنِّي
Ba ni da fuskar da zan fuskance Ka da ita face kyakkyawan zato na
a gare Ka ya Ubangiji, don haka ka ji kaina kada ka jarraba ni
تُبْتْ يَا رَبِّ فَاقْبَلْ تَوْبَتِي وَاعْفُ عَنِّي
وَامْحُ ذَنْبِي وَسَامِحْ كُلَّ تَقْصِيرْ مِنِّي
Na tuba ya Ubangiji, saboda haka ka karbi tubana ka yafe mini
ka kankare zunubina ka yafe kowane gazawa daga gare ni
خِفِتْ مِنْ عَاقِبَةْ أَمْرِي فَجُدْ لِي بِأَمْنِي
مَحِضْ فَضْلٍ وَإِحْسَانٍ وَجُودٍ وَمَنِّ
Ina tsoron sakamakon lamarina, don haka ka yi mini kyautar tsira
ta hanyar tsantsar falala, kyautatawa, karamci, da ni'ima
آه مِنْ عَثْرَتِي يَا رَبِّ مِنْهَا أَقِلْنِي
زَادْ ذَنْبِي وَمِنْ كُثْرِ الْخَطَا حَارْ ذِهْنِي
Kaitona daga tuntubena ya Ubangiji, ka tada ni daga gare shi
zunubina ya karu, saboda yawan kura-kurai hankalina ya rude
أَدْرِكْ أَدْرِكْ بِتَعْجِيلِ الْفَرَجْ وَانْتَقِدْنِي
وَاعْطِنِي عِلِمْ مِنْكَ يَا إِلَهِي لَدُنِّي
Ka kawo mini dauki, ka kawo mini dauki, ka gaggauta yaye mini kuncina ka tseratar da ni
ka ba ni ilimi daga gare Ka, ya Allahna, na ladunni
يَنْجَلِي بِهْ عَنِ الْقَلْبِ الْصَّدِى كُلَّ رَيْنِ
ياَ سَمِيعَ الْدُّعَاءْ سَلْكَ اسْتَجِبْ وَاسْتَمِعْنِي
Wanda dukkan tsatsa da datti za su yaye daga zuciya da shi
ya Mai jin addu’a, ina rokon Ka ka amsa mini kuma ka saurari kirana
مَا لِي إِلَّا أَنْتَ مُعْطِي
مَا لِي إِلَّا أَنْتَ مُغْنِي
Ba ni da kowa face Kai Mai bayarwa
ba ni da kowa face Kai Mai wadatarwa