صَفَتِ النَّظْرَهْ
Ganin Ya Washe
Ha
Ha
صَفَتِ النَّظْرَهْ طَابَتِ الْحَضْرَةْ
جَاءَتِ الْبُشْرَى لِأَهْل اللهِ
Duban ya tsarkaka halara ta yi dadi
Bushara ta zo ga mutanen Allah
قَامُوْا سُكَارَى لِذِي الْبِشَارَه
جَعْلَوْا عِمَارَهْ شُكْراً لِلّهِ
Sun tashi kamar bugaggu saboda bushara
Sun kafa majalisin zikiri don godiya ga Allah
أَيُّهَا الْحَاضِرْ اُذْكُرْ وَذَاكِرْ
إِيَّاكَ تُنْكِرْ حَالَ أَهْلِ اللهِ
Ya kai mai halarta ka yi zikiri ka kuma tunatar
Ka kiyayi karyata yanayin mutanen Allah
فَسَلِّمْ لَهُمْ فِيمَا عَرَاهُمْ
وَاعْلَمْ أَنَّهُمْ غَابُوْا فِي اللهِ
Ka mika wuya gare su a kan abin da ya same su
Ka sani cewa su kam sun bace a cikin Allah
فَالْوَجْدُ بِهِمْ دَاعِيْ يَدْعِيْهِمْ
يَطْرَأْ عَلَيْهِمْ فِيْ ذِكْرِ اللهِ
Domin shauki wani mai kira ne da ke kiran su
Yana bijiro musu ne yayin ambaton Allah
وَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَلْيَتَوَاجَدْ
قَصْداً يَتَعَرَّضْ لِفَضْلِ اللهِ
Wanda bai tsinci shauki ba to ya nuna shaukin
Da nufin fuskantar falalar Allah
هَكَذَا قَالُوْا وَلِذَا مَالَوْا
وَلَقَدْ غَالُوْا فِي ذِكْرِ اللهِ
Haka suka fada kuma shi ya sa suka karkata
Lallai sun zurfafa a cikin ambaton Allah
حَتَّى قَدْ ظَنَّا مَنْ لَيْسَ مِنَّا
أَنَّا جُنِنَّا بِذِكْرِاللهِ
Har sai da wanda ba namu ba ya raya a ransa
Cewa mun haukace ne saboda ambaton Allah
هَنِيْئاً لَنَا ثُمَّ بُشْرَانَا
إِنْ كَانَ لَنَا حُمْقٌ فِي اللهِ
Murna ta tabbata gare mu da kuma bushara
Idan har muna da hauka saboda Allah