يَا جَدَّ السُّلَالَةْ
Ya Kakan Tsatso
Ha
يَا جَدَّ السُّلَالَةْ
يَا مَجْمَعَ كَمَالَهْ
Ya kakan tsatstsafan nan madaukaki
Ya matattarar dukkan kamala
يَا جَمِيلًا فِي جَمَالِهْ
جَمَالُكَ لَا مِثَالَهْ
Ya mai kyau a cikin kyawunsa
Kyawunka ba shi da misali
فَائِقٌ لِلْبُدُورِ
مُقْتَبَسٌ بِنُورِهِ
Ya darara wa dukkan cikakkun watanni
An aro haskensu ne daga haskensa
مُشْتَاقٌ أَنَ أَزُورَهُ
عِنْدَهُ الدَّمْعُ سَالَا
Ina marmarin in ziyarce shi
A gareshi hawaye suke kwarara
رُؤْيَاكَ النَّبِيَّ
سَعَادَةٌ هَنِيَّةْ
Ganinka ya kai Annabi ﷺ
Wani babban rabo ne mai dadi
بِرِيحِهَا الْعِطْرِيَّةْ
فِي النَّوْمِ أَوْ خَيَالَا
Tare da iskar sa mai kamshi
Cikin barci ko a cikin mafarki
جِئْتُ لِلرِّحَابِ
وَاقِفٌ بِبَابِه
Na zo zuwa ga haraba mai alfarma
Ina tsaye a bakin kofarsa
بِمَجْمَعَ الْأَحْبَابِ
حَطَطْتُ الرِّحَالَ
A matattarar dukkan masoya
Na sauke kayan tafiyata
أَسَدٌ فَوْقَ نَارَا
حَيْدَرْ الْكَرَّارَ
Zaki ne a tsakiyar rurin wuta
Haidar mai yawan kai farmaki
كَمْ بِالسَّيْفِ صَالَ
كَمْ رَعَدَ الْجِبَالَ
Sau nawa ya yi artabu da takobi
Sau nawa ya girgiza duwatsu!
أَهْلِي وَقَبُولِي
بِالزَّهْرَا الْبَتُولِ
Burina da karbuwata suna ga
Al-Zahra mai tsantsar tsarki
يَا بِنْتَ الرَّسُولِ
بَلِّغِي الْآمَالَ
Ya 'yar Manzon Allah ﷺ
Ki sadar da dukkan muradina
بِزَيْنَبَ الْمُشَيرَةْ
وَنَفِيسَةَ الْكَبِيرَةْ
Albarkacin Zainab mai shiryarwa
Da Nafisa babbar mace
وَعَائِشَةَ الْمُنِيرَةْ
أَنْتُمْ خَيْرُ آلَ
Da Aisha mai haskakawa
Ku ne fiyayyen dangi
أِنَنَا نَوَيْنَا
عِنْدَهُ أَتَيْنَا
Lallai mu mun kudurci niyya
Kuma zuwa gareshi muka zo
يَا جَدَّ الْحَسَنَيْنِ
إِنَّ الشَّوْقُ طَالَ
Ya kakan Al-Hasan da Al-Husain
Lallai shauki ya yi nisa
قَدَّمْنَا الْهَدِيَّةَ
لِلْعِتْرَةِ الزَّكِيَّةِ
Mun gabatar da wannan kyauta
Ga tsarkakakkun iyalan Annabi
صَلَاةٌ عَلَى النَّبِيِّ
هُوَ بَاهِي الْجَمَالِ
Salati ya tabbata ga Annabi ﷺ
Shi ne mai hasken kyawun kamala