Ha
الله الله الله الله سَيَّدِي الله
الله الله الله اَلْعَظِيْمُ الله
Allah Allah Allah Allah Shugabana Allah
Allah Allah Allah Mai Girma Allah
أَيَا مُرِيْدَ اللهُ نُعِيدْ لَكْ قَوْلِ اصْغَهْ
إِذَا تَفْهَمْ قَوْلِي بِهِ تَصِلْ لِلّهْ
Ya mai neman Allah, ina maimaita maka magana ka saurara
Idan ka fahimci maganata, da ita za ka kai ga Allah
عَلَيْكَ يَا مُرِيدْ بِخَمْرَةِ التَّوْحِيدُه
وَإِنْ تَبْغِ الْمَزِيدْ فَالْغَيْرُ عَنْكَ انْسَهْ
Ya kai muredi, ka riki ruwan inabin kadaitaka
Idan kuma kana neman kari, to ka manta da kowane waninSa
فَاذْكُرْ الاسْمَ الْأَعْظَمْ وَاطْوِ الْكَوْنَ تَغْنَمْ
وَخُضْ بَحْرَ الْقِدَمْ فَذَاكَ بَحْرُ الله
Ka ambaci Suna Mafi Girma ka nade talikai don ka rabauta
Ka nutsa cikin tekun madawwami, domin shi ne tekun Allah
وَخُضْ بَحْرَ الْأَنْوَارْ وَالْمَعْنَى وَالْأَسَرَارْ
وَافْنِ هَذِي الدِّيَارْ يَبْلُغْ قَلْبُكْ مُنَاهْ
Ka nutsa cikin tekun haske da ma'anoni da asirai
Ka narkar da wannan gida na duniya, zuciyarka za ta kai ga burinta
وَلْتَفْنَ في الْمَعْبُودْ تَذُوقْ مَعْنَى الشُّهُودُ
إِذْ لَيْسَ ذَا الْوُجُودْ إِلَّا مِنْ نُورِ الله
Ka bace cikin Abin Bauta don ka dandani ma'anar ganun zuciya
Domin babu wannan wanzuwar face daga hasken Allah
الْمُلْكُ وَالْمَلَكُوتْ كَذَاكَ الْجَبَرُوتْ
فَكُلُهَا نُعُوتْ وَالذَّاتُ مُسَمَّاهُ
Duniyar Mulki da Malakutu da kuma Jabarutu
Dukansu siffofi ne, Shi kuwa Jati ne Abin Ambato
فَغِبْ عَنِ الصِّفَاتْ وَافْنَ في ذَاتِ الذَّاتْ
هَذِي تَلَوُّنَاتْ مَصِيرُهَا لِلِهُ
Ka bace daga siffofi ka narke cikin tsantsar Jati
Wadannan launuka ne na sauyi, makomarsu ga Allah take
إِلَيْهِ الْمُنْتَهَى وَمِنْهُ الْمُبْتَدَا
وَالْآنَ قَدْ بَدَا وَالْكَوْنُ فِي حُلَاهْ
Zuwa gare Shi ne makura kuma daga gare Shi ne mafari
Kuma a yanzu Ya bayyana, alhalin talikai na sanye da adonSa
لَهُ الْكَوْنُ مِرْآتْ وَمَظْهَرُ الصِّفَاتْ
مُحَمَّدْ نُورُ الذَّاتْ عَلَيْهِ صَلَّى الله
Talikai madubi ne gare Shi, kuma gurin bayyanar siffofinSa
Muhammadu hasken Jati ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
الْعَلَاوِيْ يَقُوْلْ قَوْلًا مِنْهُ مَقْبُولُ
تَهِيْمُ بِهِ الْعُقُولْ تَغِيبْ فِي ذَاتِ الله
Al-Alawi yana fadin magana karbabbiya
Hankula na dimauta da ita, suna bacewa cikin Jatin Allah