يَا خَلِقَا الْأَكْوَانْ بِا لْلُّطْفِ عَامِلْنِي
Ya Mahaliccin Halittu, Ka Bi Da Ni Da Lutfinka
Ha
Ha
يَا خَلِقَا الْأَكْوَانْ
بِا لْلُّطْفِ عَامِلْنِي
Ya Mahaliccin dukkan talikai
Da taushin rahamarka ka bi da ni
مَا لِيْ عَمَلْ يُرْضِيْكْ
أَنْتَ الْغَنِيْ عَنِّي
Ba ni da aikin da zai gamsar da kai
Kuma kai mawadaci ne ga barina
يَا وَاهِبَ الْإِحْسَانْ
تَقْوَاكَ أَلْهِمْنِي
Ya Mai bayar da kyautatawa
Ka kwarara tsoronka a zuciyata
قَدْ خَابَ الَّذِيْ يَعْصِيْكْ
سُبْحَانَكَ ارْحَمْنِي
Lallai wanda ya saba maka ya tabe
Tsarki ya tabbata gare ka ka yi mini rahama
يَا خَلِقَا الْأَكْوَانْ
بِا لْلُّطْفِ عَامِلْنِي
Ya Mahaliccin dukkan talikai
Da taushin rahamarka ka bi da ni
مَا لِيْ عَمَلْ يُرْضِيْكْ
أَنْتَ الْغَنِيْ عَنِّي
Ba ni da aikin da zai gamsar da kai
Kuma kai mawadaci ne ga barina
بِمَنْ حَوَى الأَنْوَارْ
وَالْفَضْلَ وَالأَسْرَارْ
Saboda wanda ya game dukkan haskoki
Da falaloli da asirrori
أَحْمَدْ ضِيَا الأَبْصَارْ
مَنْ مَدْحُهُ فَنِِّي
Ahmad hasken idanuwanmu
Wanda yabon sa shi ne fasahar rayuwata
يَا خَلِقَا الْأَكْوَانْ
بِا لْلُّطْفِ عَامِلْنِي
Ya Mahaliccin dukkan talikai
Da taushin rahamarka ka bi da ni
مَا لِيْ عَمَلْ يُرْضِيْكْ
أَنْتَ الْغَنِيْ عَنِّي
Ba ni da aikin da zai gamsar da kai
Kuma kai mawadaci ne ga barina
يَا رَبُّ يَا رَحْمَنُ
صَلِّ يَا ذَا المَنِّ
Ya Ubangiji ya Mai jinƙai
Ka yi salati ya Mai yawan kyautar falala
عَالْرُّوحِ فِي الأَبْدَانْ
وَالْنُّورِ فِي العَيْنِ
Ga ruhin da ke cikin gangar jiki
Da kuma haske da ke cikin idanuwa
يَا خَلِقَا الْأَكْوَانْ
بِا لْلُّطْفِ عَامِلْنِي
Ya Mahaliccin dukkan talikai
Da taushin rahamarka ka bi da ni
مَا لِيْ عَمَلْ يُرْضِيْكْ
أَنْتَ الْغَنِيْ عَنِّي
Ba ni da aikin da zai gamsar da kai
Kuma kai mawadaci ne ga barina
مَا شَعْشَعَتْ أَنْوَارْ
مِنْ رَوْضَةِ الْمُخْتَارْ
Matuƙar haskoki suna ruruwa
Daga fadamar fiyayyen halitta
وَغَرَّدَتْ أَطْيَارْ
تَشْدُو عَلَى الغُصْنِ
Kuma tsuntsaye suna rera waƙa
Suna rera zaƙi a kan rassan bishiya