بِفَاطِمَةْ قَدْ صَفَا حَالِي
Da Faɗimat ya tsarkaka halina
Ha
Ha
بِفَاطِمَةْ قَدْ صَفَا حَالِي وَنِلْتُ الْمَرَامْ
بِضْعَة مُحَمَّدْ حَبِيبِ اللهْ خَيْرِ الْأَنَامْ
Ta dalilin Fatima halina ya tsarkaka kuma na kai ga burina
Sashen jikin Muhammad, masoyin Allah, mafi fikon halitta
أَعْلَى لَهَا اللهْ قَدْراً فِي الْعُلَا وَالْمَقَامْ
نِعْمَ الْبَتُولْ الْرَّضِيَّةْ نُورْ كُلِّ الْظَّلَامْ
Allah ya daukaka darajarta da matsayinta a madaukakin koli
Madalla da mai kamun kai, yardacciya, hasken dukkan duhu
أُمِّ الْحَسَنْ وَالْحُسَيْنْ أَهْلِ الْمَرْقَى الْعِظَامْ
لَهُمْ عَطَايَا مِنَ الْمَوْلَى كِبَارٌ جِسَامْ
Mahaifiyar Hasan da Husaini, ma'abota daukaka mai girma
Suna da kyaututtuka daga Ubangiji, manya kuma masu kima
هُمْ سَادَةَ أَهْلِ الْجِنَانِ الْعَالِيَةْ يَا غُلَامْ
مَنْ حَبَّهُمْ صِدِقْ بَا يِسْكُنْ بِدَارِ الْسَّلَامْ
Su ne shugabannin ma'abota aljannun koli, ya kai yaro
Wanda ya so su da gaske zai zauna a gidan amani
وَمَنْ تَعَلَّقْ بِهِمْ يَظْفَرْ بِنَيْلِ الْمَرَامْ
أَكْرَمْتِ يَا بِضْعَةَ أَحْمَدْ فَانْعَمِي بِالْتَّمَامْ
Wanda ya rataya da su zai kai ga nasarar samun bukata
Ke mai karamci ce ya sashen jikin Ahmad, ki cika mana falala
وَامْنَحِي عَبْدَكُمْ فِي الْقُرْبْ أَعْلَى وِسَامْ
نَقُومْ بِحَمِلْ الْرَّيَاتِ الْهُدَ أَحْسَنْ قِيَامْ
Ki ba bawan naku babban lambar yabo ta kusanci
Domin mu dauki tutocin shiriya yadda ya kamata
تَعُمْ دَعْوَتُهْ فِي الْأَكْوَانْ كُلِّ الْأَنَامْ
نِلْبَسْ خِلَعْ إِرْثْ مَا يَصِفْ سَنَاهَا كَلَامْ
Domin kiran Annabi ya game kowa a cikin dukkan halittu
Kuma mu sanya tufafin gadon Annabta wanda haskensa ya fi gaban bayani
يَا نُورْ قَلْبِي وَيَا أُمِّي عَلَيْكِ الْسَّلَامْ
فِي كُلِّ حَالٍ وَشَأْنٍ كُلِّ لَحْظَةْ دَوَامْ
Ya hasken zuciyata kuma ya mahaifiyata, amincin Allah ya tabbata gare ki
A kowane hali da lamari da kowane lokaci har abada
عَلَيْكِ صَلَّى إِلَهِي مَعَ أَبِيكِ الْإِمَامْ
إِمَامْ كُلِّ الْوَرَى فِي كُلِّ خَاصٍّ وَعَامْ
Allah ya yi salati gare ki tare da mahaifinki shugaba
Jagoran dukkan halittu baki daya, zababbu da talakawa
الْشَّافِعِ الْمُبْتَغَ يَوْمَ الْلِّقَاءْ وَالْزَّهَامْ
يَوْمِ الْمَلَائِكْ تُنَادِي جَمِعْ كُلِّ الْأَنَامْ
Mai ceton da ake nema a ranar haduwa da dandazon tunkuda
Ranar da mala'iku za su yi kira ga dukkan jama'a
غُضُّوا أَبْصَارَكُمْ تَمُرْ بِنْتِ الْنَّبِيِ بِالْسَّلَامْ
وَنَكِّسُوا رُؤُوسَكُمْ مَا أَعْظَمَهْ وَاللهْ مَقَامْ
Ku sunkuyar da idanunku diyat Annabi za ta wuce cikin aminci
Kuma ku sunkuyar da kawunanku, wallahi wannan matsayi ya kai girma
تِذَكَرِينِي مَعَكِ أَعْبُرْ وَمَنْ لَهُ ذِمَامْ
حَاشَاكِ يَا أُمَّنَا تِنْسِينْ هَذَا الْغُلَامْ
Ki tuna da ni domin in ketara tare da ke a karkashin kulawarki
Ba zai taba kasancewa ba ya uwarmu ki mance da wannan yaro naki
مَحْسُوبَكُمْ يَرْتَجِيهْ مِنْكُمْ بِهِ الْإِهْتِمَامْ
أَنْتُمْ مَرَامُهْ وَمَقْصُودُهْ وَنِعْمَ الْمَرَامْ
Dan naku yana fatan samun kulawarku gare shi
Ku ne burinsa da muradinsa, kuma madalla da wannan buri
يَا بِنْتَ طه فُؤَادِي فِي مَحَبَّتِكْ هَامْ
وَاللهْ أَنْتُمْ مُرَادِي فِي الْدُّنَا وَالْقِيَامْ
Ya diyat Taha zuciyata ta birkice a cikin sonki
Wallahi ku ne muradina a duniya da ranar kiyama
وَمَا أَنَا إِلَّا بِكُمْ يَا سَادَتِي يَا كِرَامْ
عَلَيْكِ مَعَ وَالِدِكْ أَزْكَى الْصَّلَاةْ وَالسَّلَامْ
Ni ba kowa ba ne idan ba ku ba ya shugabannina masu karamci
Aminci da gaisuwa mafi tsarki su tabbata gare ki tare da mahaifinki
وَأَهْلِ الْكِسَاءْ وَأَهْلِ بَيْتِهْ عَالِيِّينَ الْمَقَامْ
وَالْصَّحْبْ أَجْمَعْ وَمَنْ عَلَى هُدَاهْ اِسْتَقَامْ
Da ma'abota bargo da mutanen gidansa masu daukakar matsayi
Da sahabbai baki daya da duk wanda ya dore a kan shiriyarsa