مَنْ مِثْلُ أحمد
Waye kamar Ahmad?
Ha
اللهْ اللهُ اللهْ اللهُ
اللهْ اللهُ تَبَارَكَ اللهُ
Allah Allah, Allah Allah
Allah Allah, Allah Mai albarka ne
مَنْ مِثْلُ أَحْمَدَ فِي الكَوْنَيْنِ نَهْوَاهُ
بَدْرٌ جَمِيعُ الوَرَى فِي حُسْنِهِ تَاهُوا
Wane ne kamar Ahmad a gidan duniya da lahira?
Cikakken wata wanda talikai suka bace a cikin kyawunsa
مَن مِثْلُهُ وَ إِلَهُ الْعَرْشِ شَرَّفَهُ
بِالْخَلْقِ وَ الْخُلْقِ إِنَّ اللَّهَ أَعْطَاهُ
Wane ne tamkarsa alhalin Ubangijin Al’arshi ya girmama shi?
A halitta da dabi’u, hakika Allah ya ba shi
وَالشَّمْسُ تَخْجَلُ مِنْ أَنْوَارِ طَلْعَتِهِ
حَارَتْ عُقُولُ الْوَرَى فِي فَهْمِ مَعْنَاهُ
Rana tana jin kunya daga hasken fitowarsa
Hankula sun rude wajen fahimtar hakikaninsa
تَبَارَكَ اللَّهُ مَا أَحْلَى شَمَائِلَهُ
حَازَ الْجَمَالَ فَمَا أَبْهَى مُحَيَّاهُ
Tsarki ya tabbata ga Allah, maza dadi halayensa suke
Ya tattara kyakkyawa, maza hasken fuskarsa yake
يَا عُرْبَ وَادِي النَّقَى يَا أَهْلَ كَاظِمَةٍ
فِي حَيِّكُمْ قَمَرٌ فِي الْقَلْبِ مَثْوَاهُ
Ya Larabawan kwarin Nuqa, ya mutanen Kadhima
A unguwarku akwai wata da wurin zamansa yake a zuciya
صَلَّى عَلَيْهِ إِلَهُ الْعَرْشِ مَا طَلَعَتْ
شَمْسٌ وَ مَا حَدْحَدَ الْحَادِي مَطَايَاهُ
Amincin Ubangijin Al’arshi ya tabbata gare shi muddin rana tana fitowa
Babu rana ko jagora da ya yi daidai da tafarkinsa
اللهُ بِالْمَدْحِ لِلْمُخْتارِ مَنَّ عَلَيّْ
عَسَى يُرى لِيَ بَيْنَ المَادِحِيْنَ حَلَي
Allah ya yi mini falala da yabon Zababbe
Ina fatan a ganni a cikin masu yabon sunansa
إِذَا أَتَيْتُ لِأَقْرَا الصُّحْفَ مِنْ عَمَلِيْ
مَالِي سِوَى مَنْ لَهُ فَضْلٌ يُشِيْرُ إِلَىّ
Idan na zo karanta kundin ayyukana
Ba ni da kowa sai Mai falala, wanda yake karkatar da rahamarSa gare ni
مُحَمَّدٌ سَيِّدُ الكَوْنَيْنِ وَالثَّقَلَيْـنِ
وَالفَرِيقَيْنِ مِنْ عُرْبٍ وَمِنْ عَجَمِ
Muhammad shugaban gidaje biyu ne, da na aljanu da na mutane
Da kungiyoyi biyu na Larabawa da wadanda ba Larabawa ba
هُوَ الحَبِيبُ الذِّي تُرْجَى شَفَاعَتُهُ
لِكُلِّ هَوْلٍ مِنَ الأَهْوَالِ مُقْتَحَمِ
Shi ne abin kauna wanda ake fatan cetonsa
Daga kowane firgici na mawuyatan abubuwan da ke aukuwa
نَبِيُّنَا الآمِرُ النَّاهِي فَلاَ أَحَدٌ
أَبَرَّ فِي قَوْلِ لاَ مِنْهُ وَلاَ نَعَمِ
Annabinmu mai umarni da hani, babu wani wanda
Ya kai shi gaskiyar magana, walau na 'a'a ko na 'e'
كَالزَّهْرِ فِي تَرَفٍ وَالبَدْرِ فِي شَرَفٍ
وَالبَحْرِ فِي كَرَمٍ وَالدَّهْرِ فِي هِمَمِ
Kamar fure yake a sabunta da cikakken wata a daukaka
Kamar teku a karamci da kuma zamani a karfin azama
يِا رَبِّ بِالمُصْطَفَى بَلِّغْ مَقَاصِدَنَا
وَاغْفِرْ لَنَا مَا مَضَى يَا وَاسِعَ الكَرَمِ
Ya Ubangiji, albarkacin Zababbe, Ka kai mu ga muradanmu
Ka gafarta mana abin da ya wuce, ya Mai yalwar karamci
وَاغْفِرْ إِلَهِي لِكُلِ المُسْلِمِينَ بِمَا
يَتْلُونَ فِي المَسْجِدِ الأَقْصَى وَفِي الحَرَمِ
Kuma Ka gafarta wa dukkan Musulmi, ya Ubangijina
Don abin da suke karantawa a Masallacin Aqsa da Masallaci Mai alfarma
بِجَاهِ مَنْ بَيْتُهُ فِي طَيْبَةٍ حَرَمٌ
وَإسْمُهُ قَسَمٌ مِنْ أَعْظَمِ الْقَسَمِ
Don darajar wanda gidansa a Taiba yake harami
Kuma sunansa rantsuwa ce daga cikin mafi girman rantsuwoyi