رَسُولَ إِلَهِ الْعَالَمِينَ تَعَالَى
Manzon Ubangijin talikai Madaukaki
Ha
Ha
رَسُولَ إِلَــهِ الْعَالَمِيـــــنَ تَعَالَـى
خَدِيمُكَ نَادَى يَا رَسُولُ تَعَـــالاَ
Ya Manzon Allah na Ubangijin talikai Madaukaki
Mai hidimarka ya kira, ya Manzo ka kusanto
خَدِيمُكَ نَادَى يَا رَسُولُ فَلاَ أُرَى
فَقِيرًا إِلَى غَيْــرِ الْإِلَـــهِ تَعَالَــى
Mai hidimarka ya kira ya Manzo domin kada a ganni
Matalauci ga kowa in ba Allah Madaukaki ba
خَدِيمٌ بِأَقْصَى الْغَرْبِ يَدْعُو مُحَمَّــدًا
وَلَيْسَ يَرَى غَيْرَ الْرَّسُـــولِ ثِمَـالاَ
Wani mai hidima a can karshen yamma yana kiran Muhammadu
Kuma ba ya ganin kowa in ba Manzo ba a matsayin mafaka
خَدِيمٌ ثَـوَى بِالْبَابِ وَهْــــوَ مُؤَمِّــلٌ
إِيَابًا كَرِيمًــــا وَهْـوَ جَيْــرِ أَطَــالاَ
Mai hidima ne ya dawwama a kofa yana mai cike da fata
Na samun karamcin tarba koda kuwa zamansa ya tsawaita
تَصَاغَرَ عِنْدِي غَيْرُ أَحْمَــدَ إِنَّنِــي
أُرَجِّي مِنَ الْهَــادِي الْعِبَــادِ مَنَـالاَ
Kowa ya kankance a idona in ba Ahmadu ba, domin ni
Ina fatan samun babbar falala daga Mai shiryar da bayi
كَرِيمَ الْسَّجَايَا وَاسِعَ الْجُودِ مَا تَرَى
لِضَيْـــــفِ كَرِيــمٍ قَــدْ أَجَادَ مَقَــالاَ
Ya mai kyawun halaye da yalwar kyauta, mene ne kake gani
Ga bakon wani Mai karamci, wanda ya kyautata bayanin bukatarsa
فَهَبْهُ عَلَى مِقْدَارِ كَفِّــكَ مُصْطَفَى الْ
بَرَايَــا عَطَاءً لاَ يَخَــافُ زَوَالاَ
To ka ba shi gwargwadon fadin tafin hannunka ya Zababben
Halittu, kyautar da ba ta tsoron karewa ko gushewa
فَفِي كُلِّ حَيٍّ قَدْ خَبَطْتَ بِنِعْمَــةٍ
وَإِنِّي كَشأْسٍ قَــدْ أَرُومُ نَــوَالاَ
Domin a cikin kowane rayayye ka shimfida wata ni'ima
Kuma ni ma kamar wani mai neman taimako nake kwadayin kyautarka
عَلَيْكَ صَـــلاَةُ اللّٰهِ ثُــمَّ سَلاَمُــهُ
وَتَشْمَلُ أَصْحَابَ الْنَّبِـــيِّ وَآلاَ
Dadin tsira da amincin Allah su tabbata a gare ka
Kuma su game dukkan sahabban Annabi da iyalansa