فَيَا نَفَحَاتِ اللهِ يَا عَطَفَاتِهِ
O Divine Breaths of Allah, O His Affections
Ha
فَيَا نَفَحَاتِ اللهِ يَا عَطَفَاتِهِ
وَيَا جَذَبَاتِ الْحَقِّ جُودِي بِزَوْرَةِ
Ya dukkan iskokin rahamar Allah da tausayinsa
Ya janyewar gaskiya ka yi kyauta da ziyara
وَيَا نَظَرَاتِ اللّهِ يَا لَحَظَاتِهِ
وَيَا نَسَمَاتِ اللُّطْفِ أُمِّى بِهَبَّةِ
Ya kallon rahamar Allah da kula tasa
Ya dukkan ni'imomin taushin hali ka nufo ni da garabasa
وَيَا غَارَةَ الرَّحْمَانِ جُدِّىْ بِسُرْعَةِ
إِلَيْنَا وَحُلِّى عَقْدَ كُلِّ مُلِمَّةِ
Ya agajin Mai-Rahama ka yi gaggawa
Gare mu, ka kwance kullin kowace musiba
وَيَا رَحْمَةَ الرَّبِّ الرَّحِيْمِ تَوَجَّهِىْ
وَأَحْيِىْ بِرُوْحِ الفَضْلِ كُلَّ رَمِيْمَةِ
Ya rahamar Ubangiji Mai jin kai ka fuskanto
Ka raya kowace rubabbar gaba da ruhin falala
وَيَاكُلَّ أَبْوَابِ الْقَبُولِ تَفَتَّحِىْ
فَإِنَّ مَطَايَا الْقَصْدِ نَحْوَكَ أَمَّتِ
Ya dukkan kofofin karba ku bude
Domin kuwa dabbobin nufi gare ku suka dosa
وَيَاسُحُبَ الْجُوْدِ الْإِلَهِيِّ أَمْطِرِىْ
فَإِنَّ أَكُفَّ الْمَحْلِ تِلْقَاكِ مُدَّتِ
Ya giragizen kyautar Ubangiji ku yi ruwa
Domin kuwa tafukan bukatu gare ku aka mika su
بِحُرْمَةِ هَادِيْنَا وَمُحْيِيْ قُلُوْبِنَا
وَمُرْشِدِنَا نَهْجَ الطَّرِيْقِ الْقَوِيْمَةِ
Domin alfarmar jagoranmu mai raya zukatanmu
Kuma mai nuna mana hanyar nan madaidaiciya
دَعَانَا إِلَى حَقٍّ بِحَقٍّ مُنَزَّلٍ
عَلَيْهِ مِنَ الرَّحْمَانِ أَفْضَلَ دَعْوَةِ
Ya kira mu zuwa ga gaskiya da gaskiyar da aka saukar
Gare shi daga Mai-Rahama, mafi kyawun kira
أَجَبْنَا قَبِلْنَا مُذْعِنِيْنَ لِأَمْرِهِ
سَمِعْنَا أَطَعْنَا عَنْ هُدىً وَبَصِيْرَةِ
Mun amsa mun yarda muna masu mika wuya ga umarninsa
Mun ji mun yi biyayya bisa shiriya da basira
فَيَارَبِّ ثَبِّتْنَا عَلَى الْحَقِّ وَالْهُدَى
وَيَارَبِّ اِقْبِضْنَا عَلَى خَيْرِ مِلَّةِ
Ya Ubangiji Ka tabbatar da mu akan gaskiya da shiriya
Ya Ubangiji Ka karbi ranmu akan mafi alherin addini
وَعُمَّ أُصُوْلاً وَالْفُرُوْعَ بِرَحْمَةٍ
وَأَهْلاً وَأَصْحَاباً وَكُلَّ قَرَابَةِ
Ka game iyaye da zuri'a da rahamarka
Da iyali da abokai da dukkan 'yan uwa
وَسَائِرِ أَهْلِ الدِّيْنِ مِنْ كُلِّ مُسْلِمٍ
أَقَامَ لَكَ التَّوْحِيْدَ مِنْ غَيْرِ رِيْبَةِ
Da sauran ma'abota addini daga dukkan musulmi
Wanda ya tsayar Maka da kadaitaka ba tare da shakka ba
وَصَلِّ وَسَلِّمْ دَائِمَ الدَّهْرِ سَرْمَداً
عَلَى خَيْرِ مَبْعُوْثٍ إِلَى خَيْرِ أُمَّةِ
Ka yi tsira da aminci dawwamamme har abada
Ga mafi alherin wanda aka aiko zuwa ga mafi alherin al'umma
مُحَمَّدٍ الْمَخْصُوْصِ مِنْكَ بِفَضْلِكَ
الْعَظِيْمِ وَإِنْزَالِ الْكِتَابِ وَحِكْمَةِ
Muhammadu wanda Ka kebe shi da falalarka
Mai girma, da saukar da Littafi da hikima