رَبِّي لَهُ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَى
Ubangijina Yana Da Kyawawan Sunaye
Ha
رَبِّي لَهُ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَى
تُسَبِّحْ لَهُ الْأكْوَانْ
Ubangijina gare Shi kyawawan sunaye suke
Dukkan halitta suna yi Masa tasbihi
إِلَيْهِ يَرْجِعُ كُلُّ أَمْرٍ
كُلُّ زَمَانٍ وَكُلَّ مَكَانْ
Gare Shi kowane lamari yake komawa
A kowane zamani da kowane wuri
إِذَا دَعَوْتْ فَادْعُ الْإِلَهْ
وَإِنِ اسْتَجَرْتَ فَلُذْ بِاللَّهْ
Idan za ka yi kira to ka kira Ubangiji
Idan kuma za ka nemi tsari to ka fake da Allah
مَا لَنَا مَوْلًى سِوَاهْ
عَفُوٌّ كَرِيمٌ وَرَحْمَانْ
Ba mu da wani majibinci in ba Shi ba
Shi Mai yafiya ne, Karimi, kuma Mai jinƙai
رَبِّي لَهُ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَى
تُسَبِّحْ لَهُ الْأكْوَانْ
Ubangijina gare Shi kyawawan sunaye suke
Dukkan halitta suna yi Masa tasbihi
إِلَيْهِ يَرْجِعُ كُلُّ أَمْرٍ
كُلُّ زَمَانٍ وَكُلَّ مَكَانْ
Gare Shi kowane lamari yake komawa
A kowane zamani da kowane wuri
اتَّقِ اللَّهْ وَلَهُ اِصْبِرْ
فَالْصَّبْرُ فِي الْعُقْبَى حَمِيدْ
Ka ji tsoron Allah kuma ka yi haƙuri saboda Shi
Domin haƙuri a ƙarshe abin yabo ne
وَتَزَوَّدْ عِلْمًا وَبَيَانًا
مِنَ الْسُّنَّةِ وَالْقُرْآنْ
Kuma ka yi guzurin ilimi da bayani
Daga Sunnah da kuma Alƙur'ani