خُذْ مَا صَفَا وَدَعِ الْكَدَر
Dauki Abin Da Ya Tsarkaka, Ka Bar Abin Da Ya Gurbata
Ha
Ha
يَا رَبَّنَا يَا رَبَّنَا
غِثْنَا بِقُرْبِ الـْمُصْطَفَى
Ya Ubangijinmu ya Ubangijinmu
Ka agaza mana ta kusancin Zabbabben-Ma’aiki
وَ ارْحَمْ إِلَهِي ضَعْفَنَا
بِٱلْمُصْطَفَىٰ خَيْرِ ٱلْبَشَرْ
Kuma Ka tausaya ya Ubangijina ga rauninmu
albarkacin Zabbabben-Ma’aiki, mafificin mutane
خُذْ مَا صَفَا وَدَعِ الْكَدَرْ
وَكِلِ الْأُمُورَ إلى الْقَدَرْ
Ka dauki abin da ya tsarkaka ka bar gurbatacce
ka damka dukkan al’amura ga Kaddara
مَهْمَا غُلِبْتَ كَمَا أَمَرْ
هَادِي الْوَرَى خَيْرُ الْبَشَرْ
Duk lokacin da aka rinjaye ka ka bi umarnin
Jagoran halitta, mafificin mutane
إِنَّ الْأُمُورَ جَرَى بِهَا
قَلَمٌ عَلَى الْلَّوْحِ الْأَغَرْ
Lallai dukkan al’amura sun riga sun gudana
ta hanyar alkalami a kan Allon-Kariya mai haske
فِي سَابِقِ الْعِلْمِ الْقَدِيمْ
مِنْ قَبْلِ إِيجَادِ الْصُّوَرْ
A cikin tsohon ilimi na tun fil azal
tun kafin samar da siffofin halitta
يَا رَبَّنَا يَا رَبَّنَا
غِثْنَا بِقُرْبِ الـْمُصْطَفَى
Ya Ubangijinmu ya Ubangijinmu
Ka agaza mana ta kusancin Zabbabben-Ma’aiki
وَ ارْحَمْ إِلَهِي ضَعْفَنَا
بِٱلْمُصْطَفَىٰ خَيْرِ ٱلْبَشَرْ
Kuma Ka tausaya ya Ubangijina ga rauninmu
albarkacin Zabbabben-Ma’aiki, mafificin mutane
وَدَعِ الْهُمُومَ فَإِنَّهَا
يَا صَاحِبِي مَحْضُ الْضَّرَرْ
Ka watsar da damuwoyi domin su
ya abokina, tsantsar cutarwa ne kawai
وَاغْنَمْ زَمَانَكَ وَاسْتَرِحْ
مِنْ لَوْ وَلِمْ تَلْقَ الْظَّفَرْ
Ka amfani da lokacinka ka sami hutu
daga "da" da "don me," za ka sami nasara
وَارْجِعْ إِلَى اللَّهِ إِذَا
مَالَحَّ خَطْبٌ أَوْ عَصَرْ
Ka koma ga Allah a duk lokacin da
wata masifa ta matsa maka ko ta takura ka
وَإِذَا بُلِيتَ بِمِحْنَةٍ
فَاصْبِرْ لَهَا فِيمَنْ صَبَرْ
Kuma idan aka jarrabe ka da wata masifa
to ka yi hakuri tare da masu hakuri
يَا رَبَّنَا يَا رَبَّنَا
غِثْنَا بِقُرْبِ الـْمُصْطَفَى
Ya Ubangijinmu ya Ubangijinmu
Ka agaza mana ta kusancin Zabbabben-Ma’aiki
وَ ارْحَمْ إِلَهِي ضَعْفَنَا
بِٱلْمُصْطَفَىٰ خَيْرِ ٱلْبَشَرْ
Kuma Ka tausaya ya Ubangijina ga rauninmu
albarkacin Zabbabben-Ma’aiki, mafificin mutane
مِنْ كُلِّ بَرٍّ مُوقِنٍ
مُتَوَقِّرٍ عِنْدَ الْغِيَرْ
Ka kasance cikin kowane bawa na kwarai, mai yakini
mai kwarjini yayin sauye-sauyen zamani
وَإِذَا خُصِصْتَ بِنِعْمَةٍ
فَاشْكُرْ مَعَ مَنْ قَدْ شَكَرْ
Kuma idan aka kebance ka da wata ni’ima
to ka yi godiya tare da wadanda suka yi godiya
لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينْ
تُعْطَ الْمَزِيدَ كَمَا ذَكَرْ
Ga Allah Ubangijin talikai
za a kara maka kamar yadda Ya ambata
وَاعْمَلْ لِنَفْسِكَ صَالِحًا
تَنْجُو بِهِ مِنْ كُلِّ شَرْ
Ka yi wa kanka aiki na kwarai
wanda za ka tsira da shi daga kowane sharri
يَا رَبَّنَا يَا رَبَّنَا
غِثْنَا بِقُرْبِ الـْمُصْطَفَى
Ya Ubangijinmu ya Ubangijinmu
Ka agaza mana ta kusancin Zabbabben-Ma’aiki
وَ ارْحَمْ إِلَهِي ضَعْفَنَا
بِٱلْمُصْطَفَىٰ خَيْرِ ٱلْبَشَرْ
Kuma Ka tausaya ya Ubangijina ga rauninmu
albarkacin Zabbabben-Ma’aiki, mafificin mutane
وَتَفُوزُ بِالْحُسْنَى وَبِالْــــ
ــــجَنَّاتِ دَارِ الْمُسْتَقَرْ
Za ka rabauta da kyakkyawan sakamako da
gidajen Aljannah, mazaunin tabbata
دَارِ الْبَقَا دَارِ الْنَّعِيمْ
دَارِ الْكَرَامَةِ وَالْنَّظَرْ
Gidan dawwama, gidan ni’ima
gidan karramawa da ganin Ubangiji
وَأَعِدَّ زَادَكَ لِلْمَعَادْ
مِنْ قَبْلِ يَفْجَاكَ الْحَذَرْ
Ka tanadi guzurinka don Ranar Komawa
kafin abin da kake tsoro ya riske ka ba tsammani
فَالْمَوْتُ آتٍ عَنْ قَرِيبْ
وَلَعَلَّ يَوْمَكَ قَدْ حَضَرْ
Domin mutuwa mai zuwa ce nan kusa
kuma wataila kwananka ya riga ya zo
يَا رَبَّنَا يَا رَبَّنَا
غِثْنَا بِقُرْبِ الـْمُصْطَفَى
Ya Ubangijinmu ya Ubangijinmu
Ka agaza mana ta kusancin Zabbabben-Ma’aiki
وَ ارْحَمْ إِلَهِي ضَعْفَنَا
بِٱلْمُصْطَفَىٰ خَيْرِ ٱلْبَشَرْ
Kuma Ka tausaya ya Ubangijina ga rauninmu
albarkacin Zabbabben-Ma’aiki, mafificin mutane
يَا رَبُّ أَنْتَ الْمُبْتَغَى
وَالْمُرْتَجَى وَالْمُدَّخَرْ
Ya Ubangiji Kai ne abin nema
kuma abin fata, kuma Kai ne abin tanadi
يَا رَبَّنَا فَاسْتُرْ وَسَا
مِحْ أَنْتَ أَكْرَمُ مَنْ سَتَرْ
Ya Ubangijinmu Ka suturta mu Ka kuma yafe mana
domin Kai ne mafi karamcin masu suturtawa
يَا رَبَّنَا وَانْظُرْ إِلَيـْــــ
ـــنَا أَنْتَ أَحْسَنُ مَنْ نَظَرْ
Ya Ubangijinmu Ka kalle mu da rahama
domin Kai ne mafi kyawun masu kallo
يَا رَبَّنَا وَاخْتِمْ لَنَا
بِالْخَيْرِ إِنْ حَانَ الْسَّفَرْ
Ya Ubangijinmu Ka cika mana da alheri
idan lokacin tafiyar karshe ya yi
يَا رَبَّنَا يَا رَبَّنَا
غِثْنَا بِقُرْبِ الـْمُصْطَفَى
Ya Ubangijinmu ya Ubangijinmu
Ka agaza mana ta kusancin Zabbabben-Ma’aiki
وَ ارْحَمْ إِلَهِي ضَعْفَنَا
بِٱلْمُصْطَفَىٰ خَيْرِ ٱلْبَشَرْ
Kuma Ka tausaya ya Ubangijina ga rauninmu
albarkacin Zabbabben-Ma’aiki, mafificin mutane
ثُمَّ الصَّلَاةُ عَلَى الرَّسُولْ
خَيْرِ الْبَرِيَّةِ مِنْ مُضَرْ
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzo
fiyayyen halitta daga kabilar Mudar
خَتْمِ الْنَّبِيِّينَ الْكِرَامْ
نِعْمَ الْمَصَابِيحُ الْغُرَرْ
Cikon Annabawa masu daraja
madalla da fitilu masu tsananin haske
وَآلِهِ وَاصْحَابِهِ
وَالتَّابِعِينَ عَلَى الْأَثَرْ
Da iyalansa da sahabbansa
da mabiyansu wadanda suka bi sawunsu
مَا هَبَّتِ الـــنَّسَمَاتُ بِالْــــ
ــــعَرْفِ الْمُعَنْبَرِ في الْسَّحَرْ
Muddin iskar sanyi tana kadawa tare da
kamshin turaren ambar a lokacin asuba
يَا رَبَّنَا يَا رَبَّنَا
غِثْنَا بِقُرْبِ الـْمُصْطَفَى
Ya Ubangijinmu ya Ubangijinmu
Ka agaza mana ta kusancin Zabbabben-Ma’aiki
وَ ارْحَمْ إِلَهِي ضَعْفَنَا
بِٱلْمُصْطَفَىٰ خَيْرِ ٱلْبَشَرْ
Kuma Ka tausaya ya Ubangijina ga rauninmu
albarkacin Zabbabben-Ma’aiki, mafificin mutane
أَوْ غَرَّدَتْ وُرْقُ الْحِمَى
فَوْقَ الْغُصُونِ مِنَ الْشَّجَرْ
Ko muddin tattabarun harami suna kuka
a kan rassan bishiyoyi