يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji, don su da kakan su, ka gaggauta nasara da yaye kuncin.
Ha
Ha
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
عَجِّلْ بِالْسَّعْيِ لِنَحْوِهِمِ
تَلْقَ الْرِّضْوَانَ وَتَبْتَهِجِ
Ka yi gaggawar tafiya zuwa gare su
za ka iske yardar Allah kuma ka yi farin ciki
هُمْ أَهْلُ الْبَيْتِ أَئِمَّتُنَا
فِي الْخُلْدِ لَهُمْ أَعْلَى الْدَّرَجِ
Su ne 'Yan Gidan Manzo shugabanninmu
a gidan dawwama suna da mafi daukakar darajoji
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
سَلِّمْ تَسْلَمْ وَانْظُرْ عَجَبًا
تِلْكَ الْأَنْوَارُ مِنَ الْفَرَجِ
Mika wuya ka tsira ka kuma kalli abin mamaki
wadancan hasken dake fitowa daga yaye kunci
وَاشْرَبْ وَاطْرَبْ وَانْشَقْ عَطِرًا
قَدْ فَاقَ شَذَاهُ عَلَى الْأَرَجِ
Ka sha ka yi nishadi ka kuma shakar kamshi
wanda kamshinsa ya zarce kowane irin turare
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
قَوْمٌ سَادُوا فِي الْخُلْدِ عَلَى
أَهْلِ الْجَنَّاتِ أُولِي الْسُّرُجِ
Mutane ne da suka shugabanci gidan dawwama
a kan mutanen Aljanna ma'abota fitilu
وَلَهُمْ جَاهٌ وَبِجَدِّهِمُ
يَنْجُو مَنْ زَارَ فَذَاكَ نُجِي
Suna da babban matsayi kuma saboda kakaninsu
wanda ya ziyarce su ya tsira tabbas an tseratar da shi
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
أَبْشِرْ إِنْ جِئْتَ لِدَارِهِمُ
قَدْ فُزْتَ سَرِيعًا بِالْفَرَجِ
Yi bushara idan har ka zo gidansu
tabbas ka yi nasara cikin sauri ga samun yaye kunci
سَادُوا الْأَقْطَابَ لَهُمْ شَرَفٌ
يُضْوِي كَالْشَّمْسِ لَدَى الْمُهَجِ
Sun zarce dukkan Waliyyai suna da daraja
dake haskawa kamar rana a cikin rayuka
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
اِذْهَبْ بِالْلَّيْلِ لِرَوْضَتِهِمْ
أَقْدِمْ أَسْرِعْ بِالْحُبِّ وَجِي
Tafi da daddare zuwa ga lambunsu
ka gabata ka yi gaggawa da soyayya sannan ka iso
أَخْلِصْ لِلهِ بِزَوْرَتِهِمْ
أَخْلِصْ فِي الْسَّيْرِ بِلَا عِوَجِ
Yi ikhlasi ga Allah wajen ziyararsu
ka tsarkake niyya a tafiyar taka ba tare da karkata ba
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
رَاقِبْ لِلْنَّفْسِ وَشَهْوَتِهَا
إِيَّاكَ تُصَاحِبُ لِلْهَمَجِ
Ka sanya ido ga ranka da kuma sha'awace-sha'awacenta
kada ka kuskura ka abota da mutanen banza
اِعْرِفْ قَدْرَ الْأَحْبَابِ وَكُنْ
عِنْدَ الْأَحْبَابِ أُولِي الْدَّرَجِ
Ka san darajar masoya kuma ka kasance
a wurin masoyan nan ma'abota daukakar darajoji
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
وَاسْمَعْ مِنْهُمْ مَا تَسْمَعُهُ
إِنْ كُنْتَ سَمِيعًا وَابْتَهِجِ
Ka saurari abin da kake ji daga gare su
idan har kai mai saurare ne na gari sannan ka yi murna
فَهُنَاكَ لِرُوحِكَ أَسْرَارٌ
تَخْفَى الْأَسْرَارُ عَلَى السَّمِجِ
Domin a can akwai asirai ga ruhinka
asiran da suke boye ga wanda ba shi da sanin ya kamata
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
وَلِأَهْلِ الْحُبِّ مُعَتَّقَةً
كَأْسُ الْأَسْرَارِ بِلَا وَهَجِ
Kuma ga ma'abota soyayya akwai tsohon ruwan inabi
kofin asirai wanda ba shi da zafin kuna
فَاشْرَبْ مَا دُمْتَ مُحِبَّهُمُ
كَأْسًا تَنْهَاكَ عَنِ الْعِوَجِ
To ka sha muddin kana soyayya da su
kofin da zai hana ka karkata daga gaskiya
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
لا تَسْمَعْ قَوْلَ مُكَدِّرِهَا
أَعْدَى الأَعْدَاءِ الْمُعْتَلِجِ
وَاسْمَعْ أَقْوَالَ مُحِبِّهِمِ
كَالْشَّهْدِ بِهِ أَقْوَى الْحُجَجِ
Ka saurari maganganun masoyansu
kamar zuma take tana dauke da kwararan hujjoji
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
وَدَعِ الْإِنْكَارَ لِمُنْكِرِهِ
عَبْدٌ مَحْرُومٌ فِي لُجَجِ
Ka bar musu ga mai yin sa
bawan da aka hana wa alheri yana cikin rudani
لَوْ شَاهَدَ نُورَ أَحِبَّتِنَا
مَا أَنْكَرَ إِنْكَارَ الْلَّجَجِ
Da a ce ya ga hasken masoyanmu
da bai yi musu na taurin kai ba
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
مَا قَالَ مَقَالَةَ ذِي جَهْلٍ
مَا قَالَ مَقَالَةَ ذِي عِوَجٍ
Da bai fadi maganar jahili ba
kuma da bai fadi maganar karkatacce ba
وَصَلَاةُ اللهِ تَحِيَّتُهُ
لِلْهَادِي الْنَّاسَ إِلَى الْنَّهَجِ
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga mai shiryar da mutane zuwa ga tafarki madaidaici
يَا رَبِّ بِهِمْ وَبِجَدِّهِمِ
عَجِّلْ بِالْنَّصْرِ وَبِالْفَرَجِ
Ya Ubangiji saboda su da kakaninsu
ka gaggauta mana da nasara da yaye kuncin rai
وَالْآلِ جَمِيعًا سَادَتِنَا
أَهْلِ الْتَّوْفِيقِ إِلَى الْبَلَجِ
Da kuma dukkan Alayen Manzo shugabanninmu
ma'abota dacewa zuwa ga bayyanar gaskiya
مَا (صَالِحُ) يَتْلُو أَمْدَاحًا
تَضْوِي لَيْلًا مِثْلَ الْسُّرُجِ
Muddin Salihu yana karanta yabo
dake haskaka dare kamar fitilu