لِي فِي المَدِينَةِ أَحْبَابٌ إِذَا نَظَرُوا
I Have Beloveds In Medina; When They Gaze Upon Me
Ha
لِي فِي المَدِينَةِ أَحْبَابٌ إِذَا نَظَرُوا
إِلَيَّ وَلَّتْ هُمُومِي وَانْجَلَى الضَّرَرُ
Ina da masoya a Madina wadanda idan suka dube ni
damuwata takan kauce, cutarwa kuma ta yaye.
وَأَصْبَحَ القَلْبُ فِي أُنْسٍ وَفِي فَرَحٍ
جَمٍّ وَصَاحَبَنِي التَّوْفِيقُ وَالظَّفَرُ
Zuciya takan kasance cikin debe kewa da farin ciki
mai yawa, nasara da dacewa kuma su abota da ni.
يَا أَهْلَ طَيْبَةَ هَيَّا إِنَّنِي دَنِفٌ
وَإِنَّنِي لِلَّذِي أَمَّلْتُ مُنْتَظِرُ
Ya mutanen Taiba ku hanzarta gare ni, lallai ni mai tsananin shauki ne
kuma ni mai jiran abin da nake fata ne.
جَرَتْ عَوَائِدُكُمْ أَنَّ المُحِبَّ إِذَا
نَادَاكُمُ بِلِسَانِ الحُبِّ يَنْجَبِرُ
Al'adarku ta tabbata cewa lallai masoyi idan har
ya kira ku da harshen soyayya, akan biya masa bukata.
وَالحُبُّ مِلْءُ جَنَانِي بَلْ تَجَسَّمَ فِي
شَخْصٍ عَلَى صُورَتِي إِنْ دَلَّتِ الصُّوَرُ
Soyayya ta cika zuciyata, har ma ta bayyana a
surar jikina, idan har siffofi suna bayyanawa.
يَا سَيِّدَ الرُّسْلِ أَدْرِكْنِي فَمَا بَقِيَتْ
لِي حِيلةٌ غَيْرُ حُبٍّ مِنْكَ مُدَّخَرُ
Ya shugaban manzanni ka agaza mini, domin babu wata
dabara da ta rage mini sai soyayyarka da nake tanada.
لِلَّهِ مِيلادُكَ الغَالِي الذِي سَعِدَتْ
بِهِ البَسِيطَةُ وَانْجَابَتْ بِهِ الغِيَرُ
Allah ya albarkaci haihuwarka mai daraja wadda dukkan
duniya ta yi farin ciki da ita, damuwa kuma ta yaye.
يَوْمٌ بِهِ ضَاءَتِ الدُّنْيَا فَمَا طَلَعَتْ
شَمْسٌ عَلَى مِثْلِهِ فِيهَا وَلَا قَمَرُ
Rana ce da duniya ta haskaka cikinta, ba a taba samun
rana ko wata da suka fito makamantarta ba.
تَحِيَّةٌ لَكَ مِنْ قَلْبٍ مُعَطَّرَةٌ
يَزِيدُ عَرْفَ شَذَاهَا رَوْحُكَ العَطِرُ
Gaisuwa gare ka daga zuciya mai kamshi
wadda daddadan ruhinka yake kara kamshinta.
وَقَائِلٍ لِيْ مَا تَشْتَاقُ قُلْتُ لَهُ
أَشْتَاقُ طَيْبَةَ شَوْقاً لَيْسَ يَنْحَصِرُ
Akwai mai tambayata me kake muradi? Sai na ce masa
ina muradin Taiba, muradin da ba shi da iyaka.
يَا قَائِدَ الجَوِّ أَنْزِلْنِي إِذَا لَمَعَتْ
لِعَيْنِكَ القُبَّةُ الخَضْرَاءُ وَالحُجَرُ
Ya matukin jirgin sama ka saukar da ni idan har
koren daki da dakunan gidan Annabi sun bayyana a gare ka.
هُنَاكَ أَقْصِدُ شُبَّاكَ الرَّسُولِ لِكَي    
أَسْتَغْفِرُ اللهَ حَيْثُ الذَّنْبُ يُغْتَفَرُ
A can zan nufi tagar hubbaren Manzo domin
in nemi gafarar Allah a inda ake yafe zunubi.
عَلَيْكَ صَلَاةُ اللهِ مَا تُلِيَتْ    
فِي حَفْلِ مِيلادِكَ الآياتُ والسُوَرُ
Tsira da amincin Allah su tabbata a gare ka matukar ana
karanta ayoyi da surori a taron haihuwarka.
والآلِ والصَحْبِ وَالأَتْبَاعِ قَاطِبَةً
والغَوثِ والقطبِ والأحبَابِ إذْ حَضَرُوا
Da iyalanka da sahabbai da mabiya baki daya
da Gausi da Kudbi da masoya a duk lokacin da suka halarta.