نَسِيْمْ هَبَّتْ عَلَيْنَا مِنْ حِمَى الْمُصْطَفَى
Iska mai daɗi da ta buso mana daga haramin Al-Mustafā
Ha
Ha
الله الله الله الله الله الله
اللهْ اللهْ لَا إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّٰهْ
Allah Allah Allah Allah Allah Allah
Allah Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah
الله الله الله الله الله الله
اللهْ اللهْ مُحَمَّدْ رَسُولُ ٱللَّٰهْ
Allah Allah Allah Allah Allah Allah
Allah Allah, Muhammadu Manzon Allah ne
نَسِيْمْ هَبَّتْ عَلَيْنَا مِنْ حِمَى الْمُصْطَفَى
نَسِيْمْ فِيْهَا الْهَنَا فِيْهَا الْدَّوَا وَالْشِّفَا
Iska mai dadi ta buso mana daga haramin fiyayyen halitta (Mustafa)
Iska ce mai dauke da farin ciki, magani, da kuma waraka
بِشَمِّهَا يِصْلَحْ الْظَّاهِرْ لَنَا وَالْخَفَا
يَا بَخْتُ مَنْ لِلْنَّبِي فِي كُلِّ حَالِ اقْتَفَى
Ta hanyar shakar kamshinta lahirinmu da badininmu suke gyaruwa
Ina murna ga wanda ya bi sawun Annabi a kowane hali
الله الله الله الله الله الله
اللهْ اللهْ لَا إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّٰهْ
Allah Allah Allah Allah Allah Allah
Allah Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah
الله الله الله الله الله الله
اللهْ اللهْ مُحَمَّدْ رَسُولُ ٱللَّٰهْ
Allah Allah Allah Allah Allah Allah
Allah Allah, Muhammadu Manzon Allah ne
عَلَى قَدَمْ صِدْقٍ مَعَ أَهْلِ الْهِمَمِ وَالْوَفَا
هُمُ الْرِّجَالِ الْأَكَابِرْ هُمُو هُمُو الْشُّرَفَا
Cikin tafiyar gaskiya tare da ma'abota himma da cika alkawari
Su ne manyan mazaje, lallai su ne madaukaka
هُمْ أَهْلِ الْأَسْرَارِ هُمْ أَهْلِ الْنَّقَا وَالْصَّفَا
يَا حَادِيَ اسْجَعْ فَحَالِي بِالنَّبِي قَدْ صَفَا
Su ne ma'abota boyayyun asirai da tsarkin zuciya
Ya kai mai korar rakuma rera waka! Domin halina ya yi kyau saboda Annabi
الله الله الله الله الله الله
اللهْ اللهْ لَا إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّٰهْ
Allah Allah Allah Allah Allah Allah
Allah Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah
الله الله الله الله الله الله
اللهْ اللهْ مُحَمَّدْ رَسُولُ ٱللَّٰهْ
Allah Allah Allah Allah Allah Allah
Allah Allah, Muhammadu Manzon Allah ne
إِذَا بَدَتْ عَيْنِ جُوْدِ اللهِ عَنَّا عَفَى
اللهُ حَسْبِي وَنِعْمَ الْحَسْبُ حَسْبِي كَفَى
Idan har idon karamcin Allah ya bayyana to ya yafe mana
Allah ya wadatar da ni, madalla da Mai wadatarwa, wadatarSa ta ishe ni
مِنْهُ الْمَوَاهِبْ وَمِنْهُ الْعَافِيَهْ وَالْشِّفَا
يَا وَاسِعَ الْجُوْدْ رَبِّي خَيْرِ عَافِي عَفَى
Daga gare Shi kyaututtuka suke, da lafiya da kuma waraka
Ya mai fadin karamci, Ubangijina Shi ne mafi alherin mai afuwa da yafiya
الله الله الله الله الله الله
اللهْ اللهْ لَا إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّٰهْ
Allah Allah Allah Allah Allah Allah
Allah Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah
الله الله الله الله الله الله
اللهْ اللهْ مُحَمَّدْ رَسُولُ ٱللَّٰهْ
Allah Allah Allah Allah Allah Allah
Allah Allah, Muhammadu Manzon Allah ne
اُمْنُنْ عَلَيْنَا بِرُفْقَة عَبْدِكَ الْمُصْطَفَى
اُسْلُكْ بِنَا نَهْجِ مَنْ لِهَدْيِهِ اقْتَفَى
Ka yi mana baiwar kasancewa tare da bawanKa fiyayyen halitta (Mustafa)
Ka sanya mu bi tafarkin wadanda suka bi shiryarsa
نَثْبُتْ فِيْهِ وَلِوِرِّاثِ الْنَّبِي الْخُلَفَا
بِجَاهِ أَحْمَدَ حَبِيْبِ اللهِ كَنْزِ الْوَفَا
Domin mu tabbata a kanta, mu bi halifofin da suka gaji Annabi
Albarkacin matsayin Ahmad, masoyin Allah, taskar cika alkawari
الله الله الله الله الله الله
اللهْ اللهْ لَا إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّٰهْ
Allah Allah Allah Allah Allah Allah
Allah Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah
الله الله الله الله الله الله
اللهْ اللهْ مُحَمَّدْ رَسُولُ ٱللَّٰهْ
Allah Allah Allah Allah Allah Allah
Allah Allah, Muhammadu Manzon Allah ne
عَلَيْهِ صَلَّى إِلَهِي مَا الْحَيَا وَكَفَى
وَالْآلِ وَالْصَّحْبِ مَا بَرْقِ الْسَّمَا رَفْرَفَا
Tsira da amincin Ubangijina su tabbata a gare shi matukar ana ruwan sama
Da kuma iyalansa da sahabbansa matukar walkiya na giftawa a sararin samaniya