أَنَا مَالِي فِيَّاشْ
Me Ya Shafe Ni?
Ha
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى الْمُصْطَفَى
حَبِيبِنَا مُحَمَّد عَلَيْهِ السَّلَام
Ya Allah Ka yi salati ga Zababbe
Masoyinmu Muhammad, amincin Allah ya tabbata a gare shi.
أَنَا مَالِي فِيَّاشْ آشْ عَلَيَّا مِنِّي
نَقْلَقْ مِنْ رِزْقِي لَاشْ وَالْخَالِقْ يَرْزُقْنِي
Me nake da shi na iko? Me zan iya wa kaina?
Don me zan damu da arzikina, alhali Mahalicci ne ke azurta ni?
أَنَا عَبْدُ رَبٍّ لَهُ قُدْرَةٌ
يَهُونُ بِهَا كُلُّ أَمْرٍ عَسِير
Ni bawan Ubangiji ne Mai iko
Wanda da shi kowane al'amari mai tsanani yake saukaka.
فَإِنْ كُنْتُ عَبْدًا ضَعِيفَ الْقُوَّةِ
فَرَبِّي عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِير
Idan har ni bawa ne mai raunin karfi
Ubangijina kuwa a kan kowane abu Mai iko ne.
مِنِّي آشْ عَلَيَّ وَنَا عَبْدٌ مَمْلُوكْ
وَالْأَشْيَاءْ مَقْضِيَّا مَا فِي التَّحْقِيقْ شُكُوكْ
Me zan iya wa kaina alhali ni bawa ne mallaki?
Al'amura kaddararru ne, babu shakka a kan hakan.
الْمَدَد الْمَدَد أَيَا رَسُولَ الله
وَاسْقِينَا بِالْمَدَد أَيَا حَبِيبَ الله
Agaji, agaji ya Manzon Allah
Ka shayar da mu da agaji ya Masoyin Allah.
رَبِّي نَاظِرْ فِيَّا وَنَا نَظَرِي مَتْرُوكْ
فِي الْأَرْحَامْ وَالْأَحْشَا مِنْ نُطْفَةٍ صَوَّرْنِي
Ubangijina Yana kallo na, nawa ganin kuwa ba shi da amfani
A cikin mahaifa da hanji, daga digon ruwa Ya siffanta ni.
يَقُولُ لِمَا شَاءَ كُنْ فَيَكُونُ وَيُبْدِعُ سُبْحَانَهُ وَيُعِيد
وَيَحْكُمُ فِي خَلْقِهِ مَا يَشَاءُ وَيَفْعَلُ فِي مُلْكِهِ مَا يُرِيد
Yana cewa ga abin da Ya so "Kasance" sai ya kasance, Yana farar halitta sannan Ya mayar da ita
Yana yin hukunci a halittarSa yadda Ya so, kuma Yana aikata abin da Ya so a mulkinSa.