يَا وَاهِبَ الْإِنْسَانِ أَسْبَابَ الْهُدَى
Ya Mai ba wa dan Adam hanyoyin shiriya
Ha
يَا وَاهِبَ الْإِنْسَانِ أَسْبَابَ الْهُدَى
يَا مَنْ بِحَمْدِ الْعَالَمِينَ تَفَرَّدَا
Ya Mai bai wa mutum hanyoyin shiriya
Ya wanda Ya kebanta da yabon dukkan talikai
لِي عِنْدَ بَابِكَ يَا إِلَهِي دَعْوَةٌ
فِيهَا رَجَاءُ الْعُمْرِ جَاءَ مُجَسَّدَا
A kofarka ya Ubangijina ina da wata addu’a
Wanda a cikinta fatan dukkan rayuwa ya bayyana
أَنْتَ الَّذِي مَا خَابَ عِنْدَكَ سَائِلٌ
أَيَكُونُ بَابُكَ دُونَ سُؤْلِي مُؤْصَدَا
Kai ne wanda mai roko ba ya taba tawaye a gare Ka
Shin kofarka za ta kasance a rufe ga bukatata?
فَبِفَضْلِكَ اللَّهُمَّ عِشْتُ مُوَحِّدا
أَيُرَدُّ عِنْدَكَ مَنْ أَتَاكَ مُوَحِّدَا
Da falalarka ya Allah na rayu ina mai kadaita Ka
Shin za a kora wanda ya zo gare Ka yana mai kadaita Ka?
سُؤْلِي كَذَاتِكَ وَاحِدٌ فَبِحَقِّهَا
لَوْ لَحْظَةً دَعْنِي أُشَاهِدَ أَحْمَدَا
Bukatata daya ce kamar yadda Zatinka Yake guda; don haka don wannan kadaitakar
Ko na kifawar ido ne, Ka bar ni in ga Ahmad