صَلَاةُ الْبَدْرِيَّة
Salatin Badriyya
Ha
صَلَاةُ اللّٰه سَلَامُ اللّٰه
عَلَىٰ طٰهٰ رَسُولِ اللّٰه
Tsira da amincin Allah
su tabbata ga Daha Manzon Allah
صَلَاةُ اللّٰه سَلَامُ الله
عَلَىٰ يٰسٓ حَبِيبِ الله
Tsira da amincin Allah
su tabbata ga Yasin masoyin Allah
تَوَسَّلْنَا بِبِسْمِ الله
وَبِالْهَادِي رَسُولِ الله
Mun yi tawassuli da sunan Allah
da kuma Manzon Allah mai shiryarwa
وَكُلِّ مُجَاهِدٍ لِلّٰه
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا الله
Da dukkan mai jihadi saboda Allah
don darajar mutanen Badr ya Allah
إِلَهِي سَلِّمِ الْأُمَّةْ
مِنَ الْآفَاتِ وَالنِّقْمَةْ
Ya Ubangijina Ka tsarsar da al'umma
daga masifu da kuma ukuba
وَمِنْ هَمٍّ وَمِنْ غُمَّةْ
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا الله
Da kuma damuwa da bacin rai
don darajar mutanen Badr ya Allah
إِلَهِي نَجِّنَا وَاكْشِفْ
جَمِيعَ أَذِيَّةٍ وَاصْرِفْ
Ya Ubangijina Ka tseratar da mu Ka yaye mana
dukkan cutarwa sannan Ka tunkude
مَكَائِدَ الْعِدَا وَالْطُفْ
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا الله
Makircin makiya da tausayawarka
don darajar mutanen Badr ya Allah
إِلَهِي نَفِّسِ الْكُرَبَا
مِنَ الْعَاصِينَ وَالْعَطْبَا
Ya Ubangiji Ka yaye mana kuncin rayuwa
daga masu saba maka da halaka
وَكُلِّ بَلِيَّةٍ وَوَبَا
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا الله
Da dukkan bala'o'i da annoba
don darajar mutanen Badr ya Allah
فَكَمْ مِنْ رَحْمَةٍ حَصَلَتْ
وَكَمْ مِنْ ذِلَّةٍ فَصَلَتْ
Da yawa rahamomi sun tabbata
kuma da yawa kaskanci ya kauce
وَكَمْ مِنْ نِعْمَةٍ وَصَلَتْ
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا الله
Kuma da yawa ni'imomi sun iso
don darajar mutanen Badr ya Allah
وَكَمْ أَغْنَيْتَ ذَا الْعُمْرِ
وَكَمْ أَوْلَيْتَ ذَا الْفَقْرِ
Da yawa Ka wadatar da masu yawan shekaru
kuma da yawa Ka azurta talakawa
وَكَمْ عَافَيْتَ ذَا الْوِزْرِ
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا الله
Kuma da yawa Ka warkar da masu zunubi
don darajar mutanen Badr ya Allah
لَقَدْ ضَاقَتْ عَلَى الْقَلْبِ
جَمِيعَ الْاَرْضِ مَعَ رَحْبِ
Hakika duniya ta yi kunci ga zuciya
duk da fadin da take da shi baki daya
فَانْجُ مِنَ الْبَلَا الصَّعْبِ
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا الله
Saboda haka Ka tserar da mu daga bala'i mai tsanani
don darajar mutanen Badr ya Allah
أَتَيْنَا طَالِبِي الرِّفْقِ
وَجُلِّ الْخَيْرِ وَالسَّعْدِ
Mun zo muna neman tausayawa
da kuma dukkan alheri da farin ciki
فَوَسِّعْ مِنْحَةَ الْأَيْدِي
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا الله
Saboda haka Ka fadaɗa kyautar da kake ba mu
don darajar mutanen Badr ya Allah
فَلَا تَرْدُدْ مَعَ الْخَيْبَةْ
بَلِ اجْعَلْنَا عَلَى الطَّيْبَةْ
Kada Ka mayar da mu muna masu tawaya
a'a Ka tabbatar da mu a kan alheri
أَيَا ذَا الْعِزِّ وَالْهَيْبَةْ
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا الله
Ya Ma'abucin daukaka da kwarjini
don darajar mutanen Badr ya Allah
وَإِنْ تَرْدُدْ فَمَنْ نَأْتِي
بِنَيْلِ جَمِيعِ حَاجَاتِي
Idan Ka kore mu to wajen wa za mu tafi
don samun dukkan bukatunmu
أَيَا جَالِي الْمُلِمَّاتِ
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا الله
Ya Mai yaye dukkan damuwoyi
don darajar mutanen Badr ya Allah
إِلَهِي أَغْفِرْ وَأَكْرِمْنَا
بِنَيْلِ مَطَالِبٍ مِنَّا
Ubangijina Ka gafarta mana Ka girmama mu
ta hanyar amsa bukatunmu
وَدَفْعِ مَسَاءَةٍ عَنَّا
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا اَللّٰه
Da kuma tunkude mummuna daga gare mu
don darajar mutanen Badr ya Allah
إِلَهِي أَنْتَ ذُو لُطْفٍ
وَ ذُو فَضْلٍ وَ ذُو عَطْفٍ
Ubangijina Kai ne Ma'abucin taushi
da kuma falala da kuma jinkai
وَكَمْ مِنْ كُرْبَةٍ تَنْفِي
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا اَللّٰه
Kuma damuwoyi nawa ne Ka yaye
don darajar mutanen Badr ya Allah
وَصَلِّ عَلَى النَّبِي الْبَرِّ
بِلَا عَدٍّ وَلَا حَصْرٍ
Ka yi salati ga Annabi mai kyautatawa
ba tare da lissafi ko iyaka ba
وَآلِ سَادَةٍ غُرٍّ
بِأَهْلِ الْبَدْرِ يَا اَللّٰه
Da kuma zuriyarsa shugabanni masu daraja
don darajar mutanen Badr ya Allah