سَلُوا فُؤَادِي سَلُوهُ فَهْوَ يُخْبِرُكُمْ
Ask My Heart, Ask It, for It Shall Inform You
Ha
سَلُوا فُؤَادِي سَلُوهُ فَهْوَ يُخْبِرُكُمْ
عَنِّي إِذَا غِبْتُمْ إِذْ فِيهِ مَحْضَرُكُمْ
Ku tambayi zuciyata, ku tambaye ta domin za ta ba ku labari
game da ni sa'ar da kuka nisanta, domin a cikinta mazauninku yake
أَيَا بُدُورًا أَنَارَ الْكَوْنَ مَظْهَرُكُمْ
لَوْلَا تَعَلُّلُ قَلْبِي حِينَ أَذْكُرُكُمْ
Ya ku cikakkun watanni da bayyanarku ta haskaka dukkan halitta
ba don rarrashin zuciyata ba a lokacin da nake ambatonku
وَوَضْعُ كَفِّي عَلَيْهِ جَنَّ أَوْطَارًا
لَوْ شَابَ دَمْعِي بِحَارَ الْأَرْضِ أَغْرَقَهَا
Dora tafin hannuna a kanta ya sanya ta zauce don tsananin buri
da hawayena zai gauraya da tekunan duniya da ya nutsar da su
مِنْ مُقْلَةٍ حَرُّ نَارِ الشَّوْقِ أَرَّقَهَا
وَالْوَجْدُ قَسَّمَ أَحْشَائِي وَفَرَّقَهَا
Daga kwayar idon da zafin wutar kewa ya hana ta barci
shauki kuma ya rarraba hanjin cikina ya kuma tarwatsa su
لَوْ قَرَّبُوا النَّارَ مِنْ قَلْبِي لَأَحْرَقَهَا
فَهَلْ سَمِعْتُمْ بِقَلْبٍ أَحْرَقَ النَّارَا
Da za a kusantar da wuta ga zuciyata da ta kone ta
shin ko kun taba jin labarin zuciyar da ta kone wuta?