يَا أَجْمَلَ الْأَنْبِيَاء
Oh Most Beautiful of Prophets
Ha
يَا أَجْمَلَ الْأَنْبِيَاء
يَا أَكْمَلَ الْأَصْفِيَاء
Ya mafi kyaun Annabawa
Ya mafi cikalar zaɓaɓɓun bayi
يَا خَاتَمَ الرُّسْلِ مَا
أَحْلَاكَ فِي قَلْبِي
Ya cikon Manzanni yadda
Ka yi zaƙi a cikin zuciyata
يَا ذَا الَّذِي نُسْخَةُ
الْأَكْوَانِ فِيْكَ مَطْوِيَّ
Ya wanda dukkan tsarin
Halittu yake nannade a cikinka
عَطِيَّةٌ أَزَلِيَّة
Kyauta ce ta azal tabbatacciya
أَنْتَ الَّذِي أُعْطِيتَ
الشَّفَاعَةَ الْوَافِيَّة
Kai ne wanda aka ba wa
Wancan ceto cikakke
وَ الْخَلْقُ حِينَئِذٍ
يَلْتَمِسُونَ الْأَنْبِيَاءْ
Kuma halittu a wancan lokaci
Suna neman ceton Annabawa
ثُمَّ يُقَالُ لِلْأَنَامْ
قَدْ نِلْتُمُ الْأُمْنِيَّة
Sannan sai a ce wa talikai
Kun riga kun kai ga fatanku
أَلَا اقْصِدُوْا مُحَمَّدًا
بَابَ الْإِلَهِ الْعَالِيَ
Ku nufi Muhammadu
Ƙofar Ubangiji Maɗaukaki
آيَاتُهُ شَافِيَة
Ayoyinsa masu warkarwa ne
وَهُوَ الْمُعَدُّ لَهَا
وَ ذُوَ الْثَنَاءِ الْوَافِيَ
Shi ne wanda aka tanada dominta
Kuma ma'abucin yabo cikakke
ثُمَّ يُنَادِي سَاجِدًا
يَا رَبِّ جُدْ رَاضِيَـا
Sannan zai yi kira yana mai sujada
Ya Ubangiji Ka yi kyauta kana mai yarda
يُنَادِي اشْفَعْ يَا حَبِيْبِ
يَا صَفْوَةَ الْأَصْفِيَاءْ
Za a kira shi: Yi ceto ya Masoyina
Ya zaɓaɓɓen zaɓaɓɓu
وَسَلْ تُعْطَى مَا تَرُوْم
وَلَا تَدَعْ عَاصِيَا
Tambaya za a ba ka abin da kake nema
Kuma kada ka bar mai saɓo ko ɗaya
يَا صَفْوَةَ الْأَصْفِيَاءْ
Ya zaɓaɓɓen zaɓaɓɓu
صَلُّوْا عَلَى مَنْ عَلَا
فَوْقَ السَّمَا رَاقِيَا
Ku yi salati ga wanda ya ɗaukaka
Sama da sammai yana mai hawa
هذَا حَبِيْبٌ غَدًا
عَنَّا العَنَـا مَـاحِيَا
Wannan shi ne masoyin da gobe
Zai shafe mana dukkanin wahalhalu
يَا رَبَّنَا عَطَّفْ عَلَيْنَا
قَلْبَهُ الزَّاكِيَا
Ya Ubangijinmu Ka karkato mana
Da zuciyarsa mai tsarki gare mu
وَاخْتِمْ لَنَا خِتَامَ مِسْكٍ
يَا مُجِيْبَ الدَّاعِيَا
Ka cika mana rayuwa da miski
Ya mai amsa kiran mai kira
بِالْأَسْرَارِ الذَّاتِـيـــة
Don alfarmar asirai na Zati