هَذَا الْمَقَامُ الَّذِي لَاذَتْ بِهِ الْأُمَمُ
Wannan shi ne matsayin da al'ummai suka nemi mafaka a gare shi.
Ha
هَذَا الْمَقَامُ الَّذِي لَاذَتْ بِهِ الْأُمَمُ
وَأَذْعَنَتْ لِعُلَاهُ الْعُرْبُ وَالْعَجَمُ
Wannan shi ne matsayin da dukkan al'ummai suka fake da shi
Larabawa da wasunsu kuma suka miƙa wuya ga ɗaukakarsa
هَذَا مَقَامُ رَسُولِ اللَّهْ أَكْرَمُ مَنْ
جَاءَتْهُ مِنْ رَبِّهِ الْأَحْكَامُ وَالْحِكَمُ
Wannan matsayin Manzon Allah ne, mafi darajar wanda
Hukunci da hikimomi suka zo masa daga Ubangijinsa
هَذَا مُحَمَّدُ الْهَادِي الَّذِي مُحِيَتْ
عَنَّا بِنُورِ هُدَاهُ الْظُّلْمُ وَ الْظُّلَمُ
Wannan Muhammadu ne mai shiryarwa wanda aka shafe
Duhu da zalunci daga gare mu da hasken shiryarsa
هَذَا الَّذِي قَدْ سَمَا فَوْقَ الْسَّمَا
إِلَى مَقَامِ عِزٍّ تَنَاهَتْ دُونَهُ الْأُمَمُ
Wannan shi ne wanda ya ɗaukaka har sama da sammai
Zuwa matsayi na izza wanda sauran al'ummai suka gaza kaiwa gare shi
يَا سَيِّدِي يَا رَسُولَ اللَّهْ يَا أَمَلِي
يَا مَنْ أَلُوذُ بِهِ إِنْ زَلَّتِ الْقَدَمُ
Ya shugabana ya Manzon Allah ya abin fatana
Ya wanda nake neman mafaka gare shi idan ƙafa ta goce
بِكَ اهْتَدَيْتُ إِلَى الْإِيمَانِ فَاتَّصَلَتْ
بِذَاكَ عِنْدِي مِنْ أَفْضَالِكَ الْنِّعَمُ
Da kai ne na shiryu zuwa ga imani, hakan ya sanya
Ni'imomin falalarka suka ci gaba da kwarara gare ni
صَلَّى عَلَيْكَ إِلَهُ الْخَلْقِ مَا سَجَعَتْ
وَرْقٌ وَمَا هَطَلَتْ مِنْ سُحْبِهَا دِيَمُ
Allah Mahalicci ya yi salati a gare ka muddin
Kurciya tana rera kuka kuma giragizai suna zubar da ruwan sama