اَلـلَّـهُ يَـا اَلـلَّـه صَـلَّـى عَـلَـى الـزَّيْـن
Allah Ya Allah, ka yi salati ga mai kyau.
Ha
اَلـلَّـهُ يَـا اَلـلَّـه
صَـلْـوا عَـلَـى الْـزَّيْـنِ
Allah ya Allah
Ku yi salati ga kyakkyawan nan
طَـاطَـا الْـقَـمَـرْلِأَحْـمَـد
وَانْـشَـقَّ نِـصْـفَـيْـنِـى
Wata ya yi biyayya ga Ahmad
Ya kuma rabu gida biyu
أَبُـو بَـكْـرُ يَـا صِـدِّيـقْ
صَـاحِـبِ الْـنَّـبِـى وَرَفِـيـق
Ya Abubakar ya Siddiku
Abokin Manzo kuma amintaccensa
بِرُوحُهْ فَدَاهْ فِي الضِّيقْ
مِـنْ لَـدْغَـةِ الْـنِّـيـنِـى
Da ransa ya fanshe shi a lokacin tsanani
Saboda harbin maciji a kansa
لَـمَّـا عُـمَـرْ أَسْـلَـم
فَـرِحَ الْـنَّـبِـى وَتَـبَـسَّـم
Sa’ad da Umar ya musulunta
Annabi ya yi farin ciki ya yi murmushi
تَـبَـاشَـرَ الْإِسْـلَام
بِـدُخُـولِـهْ فِـي الْـدِّيـنِـى
Musulunci ya samu labarin farin ciki
Da shigarsa cikin addini
عُـثْـمَـانُ يَـا عُـثْـمَـان
يَـا جَـامِـعَ الْـقُـرْءَان
Ya Usman ya Usman
Ya mai tattara Alkur’ani
صِـهْـرِ الْـنَّـبِـى الْـعَـدْنَـان
زَوَّجَـهُ بِـنْـتَـيْـنِـى
Surukin Annabin nan na Adnan
Wanda ya aurar masa da ‘ya’ya mata biyu
عَـلِـىُّ يَـا كَـرَّار
سَـيْـفُـكَ طَـوِيـل بَـتَّـار
Ya Aliyu ya gwarzon mayaki
Takobinka mai tsayi ne kuma mai yanke komai
يَـا هَـازِمَ الْـكُـفَّـار
قَـتَـلَ الْـمَـلَاعِـيـنِـى
Ya mai ruguza kafirai
Wanda ya kashe tsinannu
جَـاتُـهْ الْـمُـرَبِّـيَـةْ
حَـلِـيـمَـةْ الْـسَّـعْـدِيَّـة
Mai renonsa ta zo gare shi
Halimatus Sa’adiyya
قَـالَـتْ وَهَـبُـوةْ لِـيَـا
يَـا رَبِّ هَـنِّـيـنِـى
Ta ce “Ku ba ni shi”
Ya Ubangiji Ka faranta mini da shi
جَـالُـه الْـجَـمَـل جَـالُـه
يَـزْحَـف عَـلَـى عِـقَـالُـه
Rakumi ya zo gare shi, ya zo masa
Yana rarrafe da igiyar da aka daure shi
لَـمَّـا جَـالُـه جَـمَـالُـه
سَـلِّـم عَـلَـى الـزَّيْـنِـى
Sa’ad da ya ga kyawunsa
Sai ya yi sallama ga kyakkyawan nan