حَيُّوا الْهَادِي بِأَجْمَلَ ذِكْرَى
Ku gaishe da Mai Shiryarwa da mafi kyawun ambato.
Ha
حَيُّوا الْهَادِي بِأَجْمَلَ ذِكْرَى
صَلُّوا مَعَنَا يَا حُضَّارْ
Ku gaishe da Mai Shiryarwa da mafi kyawun ambato
Ku yi salati tare da mu ya ku mahalarta
فَهُوَ عِمَادِي يَوْمَ الْمَعَادِ
نَبِيُّنَا طٰهَ الْمُخْتَارْ
Domin shi ne dogarona a ranar sakamako
Annabinmu Taha Zababben Allah
صَلُّوا مَعَنَا
Ku yi salati tare da mu
هٰذَا الَّذِي سَرَى لَيْلًا
ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّى
Wannan ne wanda ya yi tafiyar dare
Sannan ya kusanta har ya yi ƙasa-ƙasa
وَهُوَ بِالْأُفُقِ الْأَعْلَى
حَبَاهُ الْوَاحِدُ الْسَّتَّارْ
Alhali yana can saman sararin samaniya
Makaɗaici Mai Suturtawa ya yi masa kyauta
فَهُوَ عِمَادِي يَوْمَ الْمَعَادِ
نَبِيُّنَا طٰهَ الْمُخْتَارْ
Domin shi ne dogarona a ranar sakamako
Annabinmu Taha Zababben Allah
صَلُّوا مَعَنَا
Ku yi salati tare da mu
عَلَى الْعَرْشِ رَقَى الْجَمِيلْ
وَكَلَّمَهُ الْمَوْلَى الْجَلِيلْ
Zuwa ga Al’arshi kyakkyawan ya haura
Kuma Ubangiji Mai Girma ya yi masa magana
وَقَالَ أَبْشِرْ يَا خَلِيلْ
شَفَاعَتُكَ لِمَنْ تَخْتَارْ
Ya ce “Yi bushara ya masoyi”
Cetonka na wanda duk ka zaɓa ne
فَهُوَ عِمَادِي يَوْمَ الْمَعَادِ
نَبِيُّنَا طٰهَ الْمُخْتَارْ
Domin shi ne dogarona a ranar sakamako
Annabinmu Taha Zababben Allah
صَلُّوا مَعَنَا
Ku yi salati tare da mu
صَلَّى مَوْلَانَا عَلَيْهْ
وَالْآلِ وَالصَّحْبِ لَدَيْهْ
Ubangijinmu ya yi salati a gare shi
Da iyalai da sahabbai da ke tare da shi
مَنْ جَاهَدُوا بَيْنَ يَدَيْهْ
وَنَوَّرُوا لَنَا الْأَفْكَارْ
Waɗanda suka yi jihadi a gabansa
Kuma suka haskaka mana tunani
فَهُوَ عِمَادِي يَوْمَ الْمَعَادِ
نَبِيُّنَا طٰهَ الْمُخْتَارْ
Domin shi ne dogarona a ranar sakamako
Annabinmu Taha Zababben Allah
صَلُّوا مَعَنَا
Ku yi salati tare da mu