بَادِرْ لَقَدْ فَاتَتْكَ الْغَنَائِمْ
Yi maza! Lallai ganimomi sun wuce ka.
Ha
بَادِرْ لَقَدْ فَاتَتْكَ الْغَنَائِمْ
تَقَاسَمُوهَا وَأَنْتَ نَائِمْ
Yi hanzari, haƙiƙa ganimomi sun wuce ka
Sun rarraba su alhalin kana barci
وَلَوْ رَأَيْتَ الَّذِينَ فَازُوا
نُحْتَ كَمَا نَاحَتِ الْحَمَائِمْ
Da ka ga waɗanda suka sami babban rabo
Da ka yi kuka kamar yadda tantabaru ke kuka
إِنْ رُمْتَ أَلَّا تَكُونَ نَادِمْ
قُمْ لِحَبِيبِ الْقُلُوبِ لَازِمْ
Idan kana son kada ka kasance mai nadama
Tashi ka lazimci Masoyin zukata
وَلَازِمِ الْبَابَ يَا مُعْنَّى
إِنَّ الْسَّعِيدَ الَّذِي يُلَازِمْ
Ka lazimci ƙofa ya kai wanda ya wahala
Domin mai farin ciki shi ne mai dorewa a ƙofa
مَنْ لَازِمَ الْبَابَ نَالَ قُرْبا
وَفَازَ بِالْأَجْرِ وَالْغَنَائِمْ
Wanda ya lazimci ƙofa zai sami kusanci
Kuma ya yi nasara da lada da ganimomi
وَلَا تَنَمْ سَاعَةَ الْتَّجَلِّي
فَلَيْسَ يَحْظَى بِالْأَجْرِ نَائِمْ
Kada ka yi barci a sa’ar bayyanar haske
Domin mai barci ba ya samun rabo na lada
قَدْ جَرَحَتْ قَلْبِيَ الْخَطَايَا
وَلَسْتُ أَلْقَى لَهَا مَرَاهِمْ
Haƙiƙa zunubai sun raunata zuciyata
Kuma ban tsinci musu wani magani ba
سِوَى الْرِّضَا مِنْكَ يَا إِلَهِي
يَا وَاسِعَ الْجُودِ وَالْمَكَارِمْ
In ban da yardarka ya Ubangijina
Ya mai yalwar kyauta da karamci
وَقَدْ تَوَسَّلْنَا يَا إِلَهِي
بِسَيِّدِ الْعَرَبِ وَالْأَعَاجِمْ
Kuma mun yi wasila ya Ubangijina
Da shugaban Larabawa da waɗanda ba Larabawa ba
نَبِيِّنَا الْمُصْطَفَى الْتِّهَامِي
مَنْ جَاءَ لِلْأَنْبِيَاءِ خَاتَمْ
Annabinmu zaɓaɓbe ɗan ƙasar Tihama
Wanda ya zo a matsayin cikon annabawa