عَلَيْكَ صَلَّى اللهْ يَا خَيْرَ خَلْقِ اللهْ
Salatin Allah ya tabbata a gare ka, ya fiyayyen halittar Allah.
Ha
Ha
عَلَيْكَ صَلَّى اللهْ يَا خَيْرَ خَلْقِ اللهْ
وَالْآلِ وَالْأَصْحَابْ وَالْقَوْمِ أَهْلِ اللهْ
يَا كَعْبَةَ الْأَسْرَارْ وَمَنْبَعِ الْأَنْوَارْ
بِالْعَزْمِ يَا مُخْتَارْ أَيَّدْتَ دِينَ اللهْ
Ya dakin asirai kuma mabubbugar haske
Da azama ya zababben Allah ka taimaki addinin Allah
فِدَاؤُكَ الْأَرْوَاحْ وَمِثْلُهَا الْأَشْبَاحْ
يَا خِيِرَةَ الْفَتَّاحْ مِنْ أَنْبِيَاءِ اللهْ
Rayuka fansarka ne haka ma gangar jiki
Ya zababben Ubangiji Mai budewa daga cikin annabawan Allah
يَا مَنْ لَهُ الْبُرْهَانْ وَخُلْقُهُ الْقُرْآنْ
مَا كَانَتِ الْأَكْوَانْ وَحَقِّهِ لَوْلَاهْ
Ya wanda yake da hujjoji kuma dabi'unsa Alkur'ani ne
Halittu ba za su kasance ba, ina rantsuwa da gaskiyarsa, ba don shi ba
لِوَاؤُكَ الْمَرْفُوعْ وَقَوْلُكَ الْمَسْمُوعْ
وَحُبُّكَ الْمَطْبُوعْ فِي مُهْجَةِ الْأَوَّاهْ
Tutarka daukaka take kuma maganarka abin ji ce
Kuma soyayyarka tana nan kunshe a cikin zuciyar mai kuka don begenka
نَدْعُوكَ بِالسِّبْطَيْنْ لِكَشْفِ هَذَا الْغَيْمْ
يَا مَلْجَأَ الْكَوْنَيْنْ بِالْخَطْبِ بَعْدَ اللهْ
Muna kiran ka ta dalilin jikokin nan biyu domin yaye wannan bakin ciki
Ya madogarar dukkan talikai yayin tsanani bayan Allah
هَا أَنْتَ فِي الْمَحْشَرْ مُؤَيَّدُ الْمَظْهَرْ
فَكُلَّمَا تُذْكَرْ عَلَيْكَ صَلَّى اللهْ
Ga ka a filin taron kiyama ana daukaka bayyanarka
Duk sanda aka ambace ka, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ka