لِغَيْرِ جَمَالِكُمْ نَظَرِي حَرَامُ
Kallona ga wanin kyawunku haramun ne.
Ha
لِغَيْرِ جَمَالِكُمْ نَظَرِي حَرَامُ
وَغَيْرُ كَلَامُكُمْ عِنْدِي كِلَامُ
Kallon wanin kyawun ku haramun ne a gare ni
Bayan maganar ku kuma, ba ni da wata magana
وَعُمْرُ الْنَّسْرِ مِنْكُمْ بَعْضُ يَوْمٍ
وَسَاعَةُ غَيْرِكُمْ عَامٌ فَعَامُ
Tsawon ran mikiya tare da ku wani bangare ne na rana
Amma sa'a guda da wasunku shekara ce bayan shekara
وَصَبْرِي عَنْكُمُ شَيْءٌ مُحَالٌ
وَمَا لِي قَاتِلٌ إِلَّا الْفِطَامُ
Yin haƙuri da rabo da ku abu ne mai wuya
Kuma babu abin da zai kashe ni sai dai yanke ƙauna
إِذَا عَايَنْتُكُمْ زَالَتْ هُمُومِيْ
وَإِنْ غِبْتُمْ دَنَا مِنِّيْ الْحِمَامُ
Idan na gan ku dukkan damuwata takan gushe
Idan kuma kuka fake mutuwa takan matso kusa da ni
أَوَدُّ بِأَنْ أَكُونَ لَكُمْ جَلِيسًا
وَتُنْصَبَ لِي بِرَبْعِكُمُ خِيَامُ
Ina burin in kasance abokin zaman ku
A kuma kafa mini tantuna a cikin yankinku
فَدَاوُوا بِالْوِصَالِ مَرِيضَ هَجْرٍ
يَهِيمُ بِكُمْ إِذَا سَجَعَ الْحَمَامُ
Ku warkar da mara lafiyar rabuwa da maganin saduwa
Wanda yake dimauta da ku duk sa'adda kurciya ta yi kuka
حَدِيثُ غَرَامِهِ فِيكُمْ قَدِيمٌ
وَمَلْبَسُهُ مِنَ الْحُبِّ الْسِّقَامُ
Labarin tsananin ƙaunar sa gare ku tsohon lamari ne
Kuma rigar da ya sanya na soyayya ita ce rashin lafiya
فَأَنْتُمْ فِي الْأُصُولِ أَجَلُّ أَصْلٍ
إِذَا شِئْتُمْ تَحَصَّلَ لِي الْمَرَامُ
Ku ne mafificin asali a dukkan asali
Idan kuka so dukkan burina zai cika
بِكُمْ صَعْبُ الْأُمُورِ يَعُودُ سَهْلًا
فَبِالْإِحْسَانِ جُودُوا يَا كِرَامُ
Mawuyacin al'amura yana sauƙaƙa saboda ku
Don haka ku yi kyauta da karamci ya ku masu daraja
وَلَيْسَ سِوَاكُمُ لِلْجُودِ أَهْلًا
فَكَيْفَ نَزِيلُ سُوحِكُمُ يُضَامُ
Babu wanda ya cancanci yin kyauta sai ku
To ta yaya baƙo a harabar ku zai tozarta?